Iran Ta Shammaci Amurka da Isra'ila, Ta Samu Nasarar Yi Masu Illa a Yakin da Ake Yi
- Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) sun samu nasarar kakkabo wasu daga cikin kayan aikin Amurka da Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki
- Sashen tsaron sararin samaniya na IRGC ya samu nasarar kakkabowa tare da lalata wani makami mai linzami na Amurka da jirage marasa matuka na Isra'ila
- Kakkabo makaman dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fafatawa a tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Sashen tsaron sararin samaniya na rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ya kakkabo tare da lalata wani makami mai linzami na Amurka a tsakiyar kasar Iran.
Dakarun na IRGC sun kuma kakkabo wasu jirage marasa matuka guda biyu na Isra'ila sararin samaniyar Kudancin kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kara karanta wannan
Babbar Magana: Iran ta sha alwashi kan Amurka da Isra'ila ana shirin tsagaita wuta

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta Iran ta kawo rahoton nasarar da dakarun suka samu a ranar Talata, 7 ga watan Afirilun 2026.
Dakarun Iran sun kakkabo makamai
Dakarun da ke kula da sararin samaniya na IRGC ya fitar a ranar Talata (yau), sun bayyana cewa sun kakkabo tare da lalata makamin linzami nau'in AGM/158-B a sararin samaniyar kauyen Barzak, kusa da Kashan, a lardin Isfahan da ke tsakiyar kasar.
Haka zalika, sanarwar ta bayyana cewa dakarun kasar sun yi nasarar kakkabo wani jirgi mara matuki na Isra'ila nau'in Orbiter a garin Sirik da ke lardin Hormozgan a Kudancin kasar, shafin indianawaaz ya kawo labarin.
A daren jiya Litinin kuma, sashen na sararin samaniya ya kakkabo wani jirgin Amurka mara matuki nau'in MQ9 Reaper a tsibirin Qeshm da ke Kudancin Iran.
Amurka, Isra'ila na kai farmaki a Iran
Amurka da Isra'ila sun farmaki ababen more rayuwa na farar hula da wuraren samar da makamashi na Iran.

Kara karanta wannan
Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci
Hare-haren sun jawo kashe daruruwan mutanen Iran tun bayan kaddamar da yakin wuce gona da iri ba tare da tsokana ba kan Jamhuriyar Musulunci a ranar 28 ga Fabrairu.
Iran na mayar da martani kan hare-hare
Dakarun tsaron Iran sun mayar da martani da kusan jerin hare-hare 100 na ramuwar gayya, wadanda aka sanya wa lakabin "Operation True Promise 4"

Source: Twitter
Dakarun tsaron sun mayar da martani ta hanyar harba daruruwan makamai masu linzami tare da hare-haren jirage marasa matuka, kan wuraren Amurka da Isra'ila a fadin yankin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya yi babbar barazana ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi babbar barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya lashin takobin cewa da misalin karfe 8:00 na dare, agogon ET, a ranar Talata, 7 ga watan Maris 2026, zai shafe Iran daga doron duniya muddin ba a cimma yarjejeniyar buɗe mashigin tekun Hormuz ba.
Trump ya yi magana cikin kakkausar murya, har da dura ashariya, inda ya yi barazanar lalata gadaje da tashoshin wutar lantarki na Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng