Bayan Barazanar Trump, An Jero Manyan Kadarori 5 da Amurka Za Ta iya Hara a Iran
Iran – An shiga zaman dari-dari a Iran a yau Talata, 7 ga Afrilu, 2026, inda ake jiran a ga ko Donald Trump zai cika alkawarinsa na kai munanan hare-hare kan kasar.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Shugaban Amurka dai ya yi barazanar kai hare-hare kan manyan gadojin dake fadin kasar Iran, tare da dukkan manyan kadarorin kasar, ma damar ba a bude mashigar Hormuz ba.

Source: Twitter
Barazanar Donald Trump na farmakar gadojin Iran
Kafar watsa labaran Aljazeera ya gudanar da bincike kan wasu gadoji biyar da Amurka za ta iya farmaka, wadanda kai masu hari zai haifar da gagarumar asara ga Iran.
Wannan barazana na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da sojojin Amurka suka riga suka nuna karfinsu ta hanyar kai hari kan gadar B1 dake Karaj, a kasar ta Iran.
Wannan danyen aiki ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula takwas, inda masana suka kwatanta matakin a matsayin babban laifin yaki saboda nufin kai hari kan farar hula.
Gadojin da ke cikin hatsari a Iran
Masu bincike sun ayyana wadannan gadoji biyar a matsayin masu matukar muhimmanci ga Iran:
1. Gadar Lake Urmia
Wannan gadar mai tsawon kilomita 1.7 dake tsakanin jihohin Azerbaijan ta Gabas da ta Yamma, ita ce ke hada manyan biranen Tabriz da Urmia.
Farmakar wannan gadar na iya haifar da mummunar matsalar muhalli ga tafkin Urmia tare da tsayar da zirga-zirgar fararen hula.
2. Gadar The Persian Gulf
Wannan wata babbar gada ce mai tsawon kilomita 3.4 da ake kan gina wa a halin yanzu, wadda ke jihar Hormuzgan, kuma ake sa ran za ta hada tsibirin Qeshmu da babban yankin kasar. Ruguza ginshikan ta da aka kafa na iya rusa shirin Iran na shekaru da dama.
3. Gadar Karun 4 Arch
Shahararriyar gada Karun 4 Arch mai tsawon mita 378 dake jihar Chaharmahal-Bakhtiari ita ce ta hada Shahr-e-Kord da Izeh. Tarwatsa ta na iya haifar da gagarumar asara ga wani dam dake kusa da ita.

Kara karanta wannan
Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci
4. Gadar Sadr
Wannan gadar dake birnin Tehran ita ce mafi tsawo a daukacin Gabas ta Tsakiya da tsawon kilomita 11, kuma ita ce kusan ruhin zirga zirga a birnin. Hari kan gadar zai iya hallaka fararen hula da yawa da tsayar da ayyukan agajin gaggawa.
5. Gadar Ghadir
Wannan gadar dake Ahvaz tana tsakiyar yankin masana'antun mai da karfe na Iran. Ruguza wannan gadar zai iya raba birnin gida biyu da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar iyalan dake yankin, in ji rahoton NDTV.

Source: Getty Images
Tasirin barazanar Trump ga Iran
Masana sun bayyana cewa barazanar Trump na daya daga cikin dabarun "durkasa ci gaban kasa" wanda yake son aiwatar wa kan kasar Iran.
Ta hanyar ruguza gadoji da masana'antun makashi, Amurka na son durkusar da tattalin arzikin Iran gaba daya da kuma raba mazauna yankuna daban-daban da junansu.
Trump na barazanar shafe Iran daga duniya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya gargaɗi Iran cewa zai shafe gaba daya kasar daga doron kasa a daren yau muddin ba ta buɗe mashigar Hormuz ba.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi 'bazata' da za ta yi wa Amurka a yaƙi da Isra'ila bayan mata barazana
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta riga sun fara kai hare-hare kan tsibirin Kharg, wanda shi ne babban wurin fitar da man fetur na kasar Iran.
Wannan shi ne karo na huɗu da Trump yake ɗaga wa'adin kai 'mummunan hari Iran,' inda a yanzu ya ce zai shafe kasar da ƙarfe 8:00 na dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
