Labari Ya Canza, Harin da Amurka Ta Kai Tsibirin Kharg na Kasar Iran Ya Fara Zame Mata Bala'i
- Hare-haren da Amurka ta yi ikirarin kai wa tsibirin Kharg na Iran ya fara tasiri a farashin danyen man kasar a kasuwannin duniya
- Rahoto ya nuna cewa bayan bullar wannan labari, farashin danyen man Amurka ya yi tashin gwauzon zabi, inda ya kusa kai wa Dala 116
- Wannan na zuwa ne yayin da wa'adin da Trump ya gindaya na daren Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026 ya kusa cika, lamarin da ya haifar da karin fargaba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Farashin danyen man fetur na Amurka ya yi tashin gwauron zabi da fiye da kashi 3 cikin 100 yayin da kowace ganga daya ta kusa kai wa Dala 116.
Hakan ta faru ne biyo bayan rahotannin farko da suka nuna cewa Amurka ta kai hari tsibirin Kharg, inda Iran ke fitar da kashi 90 na danyen manta.

Source: Getty Images
Wani jami'in Amurka ya tabbatar wa kafar yada labarai ta NBC News kai wannan hari, sai dai ya ce hare-haren ba su shafi wuraren hakar mai ba.
Farashin gangar man Amurka ya tashi
Farashin danyen man fetur na Brent shi ma ya yi sama, inda ya haura Dala 110 a kowace ganga.
Hannun jarin Amurka (U.S. stock futures) su ma sun fadi zuwa matakin mafi kankanta a safiyar yau Talata inda jadawalin S&P 500 ya nuna faduwar fiye da kashi 0.5.
Duk ana ganin haka ta faru ne sakamakon fargabar cewa wadannan hare-hare, da wa'adin da Shugaba Donald Trump ya gindaya na karfe 8:00 na dare (agogon ET), na iya kara rura wutar rashin tabbas da karancin makamashi a kasuwannin duniya.
Harin Amurka a tsibirin Kharg
A cewar wani jami'in Amurka, dakarun kasar sun kai hari kan dinbin sansanonin sojin Iran da ke tsibirin Kharg a cikin dare.
Jami'in ya bayyana cewa aikin ya hada da hare-haren jiragen sama na yaki a gefen Arewacin tsibirin, kuma babu sojojin kasa da aka tura.
"Ba su kai hari kan man fetur ba, a maimakon haka sun farmaki rumbun ajiya na sojoji, tsarin kariya daga harin jiragen sama, da sauran gine-ginen soji,' in ji shi.
Jami'in na Amurka ya jaddada cewa dukkan wuraren da aka kai wa harin na sojoji ne, kuma yawancinsu wurare ne da Amurka ta taba farmaka a baya.
Kwanakin baya, Shugaba Trump ya taba fitowa fili ya yi ikirarin cewa cewa Amurka ta "rushe dukkan wani sansanin saoji da ke tsibirin Kharg, wanda shi ne babban abin alfaharin Iran."

Source: Getty Images
Illar da wannan farmaki ya yi wa Amurka
Tsibirin Kharg dai wata muhimmiyar mahada ce ta fitar da man fetur ga Iran, kuma a baya an yi ta rade-raden cewa zai iya zama wurin da Amurka za ta kaddamar da harin sojin kasa.
Rahoton kai hari wannan tsibiri ne ya kara jawo tashin farashin danyen mai na kasar Amurka, inda kowace ganga ta kai Dala 116, cewar tashar Al-Jazeera.
Mutanen Iran sun ba Trump mamaki
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayana tsantsar mamaki kan halin da mazauna kasar Iran ke nunawa duk da hare-haren da ake kai masu.
Donald Trump ya ce abin mamaki ne yadda wasu daga cikin ‘yan Iran ke nuna kamar ba su damu da hare-haren ba.
Trump ya sake nanata matsayarsa kan Iran, inda ya yi barazanar cewa Amurka na da karfin da za ta iya rusa kasar gaba daya cikin kankanin lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


