Babbar Magana: An Zo Gaɓa Mai 'Sarkakiya' a Tattaunawar Sulhu tsakanin Amurka da Iran

Babbar Magana: An Zo Gaɓa Mai 'Sarkakiya' a Tattaunawar Sulhu tsakanin Amurka da Iran

  • Jakadan Iran a Pakistan, Reza Amiri Moghadam ya yi bayani kan halin da ake ciki a kokarin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya
  • Reza Amiri ya ce tattaunawar Amurka da Iran kan yiwuwar tsagaita wuta ta kai wani mataki mai matukar muhimmanci da sarkakiya
  • Kasar Pakistan ce dai ta shiga tsakani domin sulhunta kasashen Amurka, Isra'ila da Iran bayan shafe fiye da wata guda ana barin wuta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Pakistan - Yunkurin da kasar Pakistan ta yi na kawo karshen yakin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai wani mataki mai matukar muhimmanci.

Idan baku manta ba Pakistan ta kara matsa kaimi a karshen makon da ya gabata domin sasanta kasashen da suka shafe sama da wata guda suna kai wa juna hare-hare.

Reza Amiri Moghadam
Jakadan kasar Iran a Pakistan, Reza Amiri Moghadam Hoto: @IranAmbPak
Source: Twitter

Tashar NBC News ta ruwaito cewa kasar ta mika daftarin tsarin tsagaita wuta ga Amurka da Iran, kuma kowace kasa ta tabbatar da cewa sakon ya isa gare ta.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Iran ta sha alwashi kan Amurka da Isra'ila ana shirin tsagaita wuta

Halin da ake ciki kan batun tsagaita wuta

Jakadan kasar Iran a Pakistan, Reza Amiri, ya tabbatar da cewa wannan kokari da ake yi da kyakkyawar niyya don dakatar da rikicin Gabas ta Tsakiya ya kai mataki mai sarkakiya.

Jakadan ya bayyana cewa kokarin da Pakistan ke yi don taimakawa wajen dakatar da yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya kai "mataki mai matukar muhimmanci da kuma sarkakiya."

A cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X a safiyar yau Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026, Jakadan Iran a Pakistan, Reza Amiri Moghadam ya yi bayanin cewa:

"Yunkuri mai kyau da amfani da Pakistan ke yi a matsayinta na mai shiga tsakani don tsagaita wuta ya kusa kaiwa ga wani mataki mai cike da sarkakiya. Ku zama cikin shiri don jin karin bayani nan ba da jimawa ba."

Ko da yake bai bayar da wasu takamaiman bayanai game da lokacin da za a fitar da sabon rahoton ba, amma ya bukaci al'umma da su zama cikin shiri don jin sakamako nan gaba kadan.

Kara karanta wannan

Ba boye boye: Iran ta bayyana matsayarta kan tsagaita wuta tsakaninta da Amurka

Mojtaba da Trump.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu, @DonaldTrump
Source: Facebook

Pakistan na taka muhimmiyar rawa

Kasar Pakistan dai tana taka muhimmiyar rawa a matsayin babbar hanyar sadarwa tsakanin Iran da Amurka a daidai lokacin da ake fadi-tashi na karshe don ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta kafin lamarin ya kara jagulewa.

A yau Talata, 7 ga Afrilu ita ce rana ta 40 da fara wannan yaki, wanda ya jawo asarar rayuka, dukiyoyi da kuma jefa duniya cikin karin matsin tattalin arziki.

Trump bai aminta da tsagaita wuta ba

A wani rahoton, kun ji cewa Fadar shugaban kasar Amurka ta ce Shugaba Donald Trump bai amince da bukatar tsagaita wuta ta kwanaki 45 da aka gabatar ba tukunna.

Sai dai bayanan da aka tattaro sun nuna cewa cewa wani jami'i a Fadar shugaban Amurka, a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2026 ya ce ana ci gaba da nazari kan batun tsagaita wutar a halin yanzu.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da musayar wuta a yakin Amurka, Isra'ila da Iran, wanda ya shafe fiye da wata daya

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262