Ana Yakin Iran, Donald Trump Ya Yi Magana kan Kim Jong Un

Ana Yakin Iran, Donald Trump Ya Yi Magana kan Kim Jong Un

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana kan Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un a wata hira da ya yi kan yakin Iran a ranar Litinin
  • Trump ya bayyana cewa Kim Jong Un ya sha yin maganganu marasa kyau ga babban abokin hamayyarsa kuma tsohon shugaban kasa, Joe Biden
  • A kwanakin baya dai Koriya ta Arewa da Jong Un ke jagoranta ta harba makamai masu linzami a cikin teku bayan jin motsin Amurka a kusa da ita

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Donald Trump ya yi ikirarin cewa shugaban Koriya ta Arewa ya yi amfani da wata kalmar batanci wajen bayyana lafiyar kwakwalwar tsohon shugaban Amurka, Joe Biden.

Rahotanni sun nuna cewa Trump da kansa ya shafe shekaru yana yi wa tsohon Shugaban Amurka, Joe Biden ba'a, musamman game da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, Shugaban Amurka ya furta abin da yake kwadayin samu daga Iran

Shugaba Donald Trump da Kim Jong Un
Donald Trump a hagu, Kim Jong Un a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Alakar Donald Trump da Kim Jong Un

Jaridar Independent ta wallafa cewa Trump ya nuna rashin jin dadinsa cewa wasu kasashe da ke da alaka da su, ciki har da Koriya ta Kudu, ba su taimaka wa Amurka a yakin da take yi da Iran ba.

Trump ya fadawa manema labarai cewa:

“Muna da sojoji 45,000 a Koriya ta Kudu don kare mu daga Kim Jong Un, wanda muke da kyakkyawar alaka da shi kamar yadda ku ka sani,”
“Ya fadi abubuwa masu kyau game da ni,”

Inji Trump game da shugaban Koriya ta Arewa.

“Ya kan kira Joe Biden da mutum mai matsalar kwakwalwa… ya ce mutum ne mai matsalar kwakwalwa. Ya yi masa mummunan suka sosai, abin ya yi muni. Amma yana son Trump.”

Sukar Kim Jong Un ga Amurka

Kim, wanda ya zama babban jagoran Koriya ta Arewa a 2011, tare da wasu manyan jami’an kasar, sun shafe shekaru suna jefa kalaman cin mutunci ga ‘yan siyasar Amurka a lokacin tashin hankali tsakanin kasashen.

Kara karanta wannan

Koriya ta Arewa ta juya wa Iran baya, an ji abin da take son kulla wa da Amurka

A 2014, mataimakin wakilin dindindin na kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Ri Tong Il, ya kira Amurka da kasar da bata tafiya a kan daidai.

A 2023, ‘yar uwar shugaban kasar, Kim Yo Jong, ta soki Biden bayan gargadinsa cewa yunkurin amfani da makamin nukiliya daga Koriya ta Arewa zai kawo karshen mulkinta.

Ta bayyana tsohon shugaban a matsayin dattijo mai raunin hankali, kuma ta ce gwamnatin kasar ta ba za ta dauki kalamansa a matsayin wani abu mai muhimmanci ba.

Shugaban Kaoriya ta Arewa
Kim Jong Un yayin gwada wani makami. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Duk da cewa Trump na yabon kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da Kim, shi ma bai tsira daga kalaman suka na shugaban Koriya ta Arewa ba.

A wa’adin mulkinsa na farko, Kim ya kira Donald Trump “tsoho mai raunin hankali,” “kare mai tsoro” da kuma “dan daba mai neman jefa kan shi a hadari.”

Ga bayanin Trump da Fox News ta wallafa a X:

Koriya ta harba makamai don jan-kunne

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Koriya ta Arewa karkashin Kim Jong Un ta harba wasu manyan makamai zuwa wani teku.

Kara karanta wannan

Raina Musulunci: An zargi Trump da kira sunan Allah a yanayi maras kyau

An ce hakan ya shafi gwaji na baya-bayan nan da ya gudana a karshen Maris, 2026 yayin da kasar ke kokarin gina makaman da za su iya kai hari zuwa nahiyar Amurka.

Koriya ta harba makaman ne bayan jin motsin dakarun Amurka a kusa da ita, lamarin da ke nuna har yanzu babu wata alaka mai kyau tsakanin kasashen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng