Bidiyo ya nuno shugaban kasar Amurka mai shekaru 78 da matarsa suna tuka kekuna a kan titi, an yi cece kuce

Bidiyo ya nuno shugaban kasar Amurka mai shekaru 78 da matarsa suna tuka kekuna a kan titi, an yi cece kuce

- An ga Joe Biden mai shekaru 78 a cikin bidiyo yana jin dadi lokacin da yake tuka keke a kan titin Amurka tare da matarsa Jill

- Shugaban na Amurka ya kasance mai kuzari yayin da yake tsere da wasu masu keke yayin da yake daga hannu ga taron jama'ar da suka kasance a wurin

- Burgewar ma’auratan a cikin bidiyon da ke yawo ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta

Shugaban kasar Amurka ya burge masu amfani da shafukan sada zumunta yayin da aka hasko shi yana gudanar da wani aiki da ba na hukuma ba.

An gano Joe Biden, a cikin wani bidiyo na Instagram da Goldmynetv ya wallafa, yana tuka keke tare da matarsa Jill Biden. Iyalan farko na Amurka sun nuna kuzari da karfi sosai duk da yawan shekarunsu yayin da suke jagorantar wasu matasa dake tuka keke tare da su.

KU KARANTA KUMA: 2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo

Bidiyo ya nuno shugaban kasar Amurka mai shekaru 78 da matar Jill suna tuka kekuna a kan titi, an yi cece kuce
Bidiyo ya nuno shugaban kasar Amurka mai shekaru 78 da matar Jill suna tuka kekuna a kan titi, an yi cece kuce Hoto: @goldmynetv
Asali: Instagram

Biden da matarsa sun yi murmushi tare da daga wa 'yan kasar da ke cikin farin ciki a wurin don ganin yadda ma'auratan ke tuka keken hannu.

An bayyana cewa ma’auratan sun yi atisayen ne don tunawa da ranar haihuwar Jill karo na 70. Hawan keke ya gudana a jihar Delaware.

'Yan Najeriya sun maida martani kan bidiyon

Bidiyon ya sami martani daban-daban daga 'yan Najeriya yayin da suke mamakin yanayin lafiyar Shugaban Amurkan da iyalinsa.

Wasu sun danganta ikonsa na hawa kan titi cikin sakewa saboda ya isar da romon dimokiradiyya ga mutanensa.

Dubi wasu martani a ƙasa:

@ i_amdoyin04 ya ce:

"Na san wani shugaban kasa da ba zai iya hawa ko da keke ba balle ya tuka daya .. Ba zan ambaci suna ba."

KU KARANTA KUMA: Stephen Akinola: Wani shahararren faston Najeriya ya mutu awanni Bayan mutuwar TB Joshua

@double_d_pedigree yayi tsokaci:

"Amma duk da haka a Afirka shuwagabannin suna rufe duk kasar saboda za su yi tafiya a kan titi."

A wani labarin, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed a ranar Litinin ya bayyana rusa ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ofisoshin 'yan sanda da sauran kayayyakin jama'a a matsayin aikin ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a Abuja a wani taro kan kare abubuwan more rayuwar jama'a, ya ce ana lalatawa tare da sace abubuwan hanyoyin jirgin kasa, layukan dogo, fitilun kan titi da sauran kayayyakin wutar lantarki, bututun mai, kayayyakin sadarwa da kayayyakin jirgin sama a kasar.

Taron ya samu halartar Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, SAN; takwaransa na Sufuri, Rotimi Amaechi; Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammed Bello, da takwaransa na jirgin sama, Hadi Sirika, a cewar Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel