Babbar Magana: Iran Ta Sha Alwashi kan Amurka da Isra'ila ana Shirin Tsagaita Wuta

Babbar Magana: Iran Ta Sha Alwashi kan Amurka da Isra'ila ana Shirin Tsagaita Wuta

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna cewa ba za ta zura ido Amurka da Isra'ila na ci gaba da kai farmaki kan wuraren da suka shafi farar hula a kasar ba
  • Kakakin hedkwatar tsaro ta Khatam al-Anbiya ya bayyana cewa tun da farko sun sanar da makiyan Iran abin da zai faru idan suka aikata hakan
  • Laftanar Kanal Ebrahim Zolfaqari ya bayyana cewa martanin zai kasance mai zafi ne kuma wanda zai girgiza makiyan kasar Iran

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha alwashi kan hare-haren da Amurka da Isra'ila suke kai mata.

Kakakin hedikwatar tsaro ta Khatam al-Anbiya ya lashi takobin cewa, duk wani kai hari kan wuraren farar hula na Iran zai fuskanci gagarumin martani mai tsanani daga dakarun tsaron ƙasar.

Kara karanta wannan

Ba boye boye: Iran ta bayyana matsayarta kan tsagaita wuta tsakaninta da Amurka

Iran ta shirya kai martani kan Amurka, Iran
Dakarun sojojin Iran na yin atisaye Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoton cewa kakakin ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Afirilun 2026.

Wani alwashi Iran ta sha kan Amurka, Isra'ila

Laftanar Kanar Ebrahim Zolfaqari ya bayyana cewa Iran za ta mayar da martani mai zafi idan aka ci gaba da farmakar wuraren fararen hula.

"Mun bayyana tun daga farkon (wannan harin da ake kai wa Iran) cewa duk wani hari kan gine-ginen farar hula zai fuskanci martani mai ƙarfi kan kadarorin makiya a yankin."

- Laftanal Kanal Ebrahim Zolfaghari

Iran za ta kai zafafan hare-hare

Ya jaddada cewa matakai na gaba na farmaki da ramuwar gayya na dakarun Iran za su kasance mafi ruguzawa da faɗaɗa idan har aka sake kai hari kan farar hula.

Kakakin ya kuma bayyana cewa asarar da maƙiyi zai tafka da barnar da za ta same shi sakamakon nacewa kan wannan salon za su ninku sosai.

Kara karanta wannan

Pakistan ta tura sako ana cikin musayar wuta, ta gabatar da matakai 2 ga Amurka da Iran

Iran na yaki da Amurka, Isra'ila

Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da wani babban hari ba tare da tsokana ba kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, inda suka kashe jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyed Ali Khamenei, da wasu manyan kwamandojin sojoji.

Iran ta gargadi Amurka, Isra'ila
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @araghchi
Source: Twitter

Hare-haren sun gudana ne duk da tattaunawar da ake yi tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

A matsayin martani, dakarun tsaron Iran sun ƙaddamar da jerin farmakin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan kadarorin Amurka a fadin Yammacin Asiya da kuma sansanonin Isra'ila.

Shirin tsagaita wuta a yakin Amurka, Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Pakistan ta gabatar da matakai biyu na yarjejeniya da nufin kawo karshen yakin da Amurka, Isra'ila suke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Bangarorin da ke cikin yakin na Gabas ta Tsakiya sun karbi daftarin yarjejeniyar kuma sun fara nazari kan wannan tsari da kasar Pakistan ta gabatar.

Babban hafsan sojojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ya tattauna da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, wakili na musamman, Steve Witkoff, da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng