An Shiga Tashin Hankali a Isra'ila da Iran Ta Harba Miyagun Makamai 10 Lokaci 1
- Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 10 a lokaci guda, a wani jerin hare-hare uku da suka firgita tsakiyar ƙasar Isra'ila yau
- Yayin da mutane ke hudun ceton rai bayan an kunna kararrawar gargadi, an rahoto cewa wata dattijuwa ta ji mummunan rauni a Tel Aviv
- Rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi amfani da sababbin makamai masu tarwatsewa tun suna a sama domin rikita shingen tsaron Isra'ila
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Isra'ila – Wani sabon tashin hankali ya ɓalle a yau Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, bayan da ƙasar Iran ta ƙaddamar da gagarumin harin makamai masu linzami kan tsakiyar ƙasar Isra'ila.
Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 10, a wani salo na yaki, wanda ta kaddamar a matakai guda uku.

Source: Getty Images
Iran ta harba makamai 10 kan Isra'ila
Wannan hari ya jawo an kunna kararrawar gargaɗi a sassan birnin Tel Aviv da kewayensa, inda aka umarci mazauna yankin da su gaggauta shiga wuraren buya, in ji rahoton Aljazeera.
Wata majiyar tsaro daga Isra'ila ta bayyana cewa:
"Iran ta yi amfani da makamai masu linzami masu tarwatsewa tun suna a sama, waɗanda ke rarraba kansu gidaje da dama kafin su fada ƙasa."
Harin ya haifar da firgici a tsakanin jama'a, inda jami'an agajin gaggawa na Isra'ila suka tabbatar da cewa wata tsohuwa mai shekaru kusan 90 ta ji rauni.
Majiyar asibiti ta bayyana cewa:
"Wata mata ta ji rauni mai tsanani sakamakon faɗuwa yayin da take gaggawar neman maɓoya lokacin da aka ji jiniyar isowar makaman."
Wuraren da makaman Iran suka fada
Rahoton jaridar Isra'ila ta Ynet News ta ruwaito cewa an tura tawagar ceto ta Magen David Adom domin binciken wurare da dama da aka cewa makaman Iran sun fada, ciki har da Aviv.

Kara karanta wannan
Wuya ta yi wuya: Isra'ila ta dakatar da kai hare hare kan kasar Iran, an ji dalili
Sauran wuraren da ake bincike kan su sun hada da Bnei Brak, Ramat Gan, Givatayim, Petah Tikva da Rosh HaAyin.
Magajin garin Ramat Gan, Carmel Shama HaCohen ya ce akwai wurare da dama da suka lalace, amma komai zai dawo daidai, yayin da wata mata ta ji rauni a Petah Tikva.

Source: Getty Images
Dabarun yaƙin Iran ta sama
Masana tsaro sun bayyana cewa yin amfani da makamai masu tarwatsewa dabara ce ta Iran domin gurgunta garkuwar Isra'ila ta Iron Dome, kamar yadda wani rahoton The Guardian ya nuna.
Waɗannan makamai suna da wahalar kakkabowa gaba ɗayansu saboda yadda suke rarrabuwa a sararin samaniya, wanda hakan ke barazana ga rayukan farar hula.
Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa sun yi nasarar kakkabo wasu daga cikin makaman, amma wasu ɓangarorinsu sun riga sun sauka a inda ba a yi tsammani ba.
Iran ta farmaki muhimmin wuri a Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Iran sun bayyana cewa sun kai hari kan masana’antun petrochemical da ke kusa da Dimona a kudancin Isra’ila.
An ce Dimona na dauke da babban cibiyar nukiliyar Isra’ila, wanda ya kara nuna muhimmancin wurin da aka kai harin wanda ya jawo mata asara.
Sanarwar ta kuma ce sojojin Iran sun kai hare-hare da jiragen mara matuki kan wuraren sojin Amurka da ke tsibirin Bubiyan a kasar Kuwait.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

