Iran Ta Sassauto, Ta Faɗi Matsayarta game da Sulhu da Amurka
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce ana jirkitar da matsayinsu a kafafen yaɗa labarai na Amurka
- Abbas Araghchi ya kuma jaddada cewa kasar Iran na son sharuddan da za su kawo ƙarshen yaƙi gaba ɗaya
- Ya gode wa Pakistan kan ƙoƙarin sasanci, yana mai cewa ba su taɓa ƙin ziyartar Islamabad ba a kan maganar sulhu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Iran – Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ana juya yadda ake gabatar da matsayar ƙasarsa kan yaƙin da ake yi a kafafen yaɗa labaran Amurka.
Abbas Araghchi ya ce rahotannin da ake fitarwa ba su nuna ainihin abin da Iran ke nema ba dangane da rikicin da ake ciki wanda Amurka da Isra'ila suka fara.

Source: Getty Images
Abbas Araghchi ya bayyana haka ne a cikin wata ƴar gajeriyar sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X yayin da Pakistan ke ƙoƙarin jawo kasashen Amurka da Iran su hau teburin sulhu.
Iran ta magantu kan rikicin Gabas ta Tsakiya
A cewar Abbas Araghchi, rahotannin da ake fitarwa ba su nuna ainihin abin da Iran ke nema ba dangane da rikicin Gabas ta Tsakiya da har yanzu ke jawo asarar rayuka.

Source: Facebook
Ya ce abin da Iran ta fi mayar da hankali a kai shi ne samun cikakken bayani da fahimta kan matsayin ƙasarta, ba tare da gurɓata shi ba.
Abbas Araghchi ya jaddada cewa Iran ba ta da wani buri face ganin an kawo ƙarshen yaƙin da ake ganin an ɗora mata ba bisa ƙa’ida ba. Iran na son ƙarshe mai ɗorewa ga yaƙi
Araghchi ya gode wa Pakistan kan rawar da take takawa wajen sasanta rikicin. Ya ce gwamnatin Iran ba ta taɓa ƙin zuwa birnin Islamabad ba domin tattaunawa. Ya ce:
"Abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne sharuddan da za su tabbatar da cikakke da ɗorewar kawo ƙarshen wannan haramtaccen yaƙi da aka ƙaƙaba mana.”
Ministan ya ƙara da cewa Iran na buƙatar yarjejeniya wacce za ta kawo ƙarshen rikicin gaba ɗaya, ba wai dakatar da shi na ɗan lokaci kawai ba.
Matsayar Iran kan sulhu da Amurka
Abbas Araghchi ya bayyana cewa irin wannan matsaya na nuna aniyar Iran na samun zaman lafiya mai ɗorewa, tare da kare muradunta na ƙasa.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a duniya kan yadda za a warware rikicin Gabas ta Tsakiya da aka fara a watan Fabarairu, 2026.
Yakin ya salwantar da rayukan bayin Allah a Iran da Isra'ila, yayin da wasu Amurkawa suka rasu a hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai kan kadarorin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Kasar Amurka ta nemi a tsagaita wuta
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun nuna kasar Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta nemi a tsagaita wuta a yakin da aka fara a karshen watan Fabrairun 2026.
Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki ana gwabza fadan da ya jawo mutuwar mutane da dama da lalata kadarorin biliyoyin Daloli a duniya.
Shugaba Donald Trump ya yi bayani game da harbo jirgin Amurka da dakarun Iran suka yi da makomar sulhun da ya ce an fara maganar shi domin a warware bakin zaren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


