Wuya Ta Yi Wuya: Isra'ila Ta Dakatar da Kai Hare Hare kan Kasar Iran, An Ji Dalili

Wuya Ta Yi Wuya: Isra'ila Ta Dakatar da Kai Hare Hare kan Kasar Iran, An Ji Dalili

  • Rundunar sojin Isra'ila ta dakatar da luguden wuta a wasu sassan Iran domin ba dakarun Amurka sararin neman matuƙan jirgin F-15E da IRGC ta harbo
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Amurka ta yi nasarar ceto guda ɗaya daga cikin matuƙan jirgin, yayin da ake ci gaba da laluben ɗayan matuƙin
  • Shugaba Donald Trump dai ya bayyana cewa kakkabo jirgin ba zai shafi tattaunawar da ake yi da Iran ba, inda ya jaddada cewa "yaƙi ne ake yi kawai"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila – Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da dakatar da kai hare-hare ta sama a wasu muhimman yankuna na ƙasar Iran a yau Juma'a, 3 ga Afrilu, 2026.

Wannan mataki ya biyo bayan kakkabo jirgin yaƙin Amurka nau'in F-15E Strike Eagle da dakarun Iran suka yi, lamarin da ya tilasta wa Amurka ƙaddamar da babban aikin ceto yau.

Kara karanta wannan

Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka, an sanya ladar kudi ga wanda ya kamo matuƙan

Isra'ila ta dakatar da hare-hare kan Iran bayan an kakkabo jirgin yakin Amurka.
An ga hasken fitar rokoki a sararin Tel Aviv a wani kokari na kakkabe makaman da Iran ta harbo. Hoto: JACK GUEZ / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta dakatar da hare-hare a Iran

Majiyoyi daga hukumar leken asiri ta Isra'ila sun tabbatar wa manema labarai cewa an ɗage wasu hare-haren da aka tsara kai wa Iran domin gudun kada a farmaki dakarun Amurka dake aikin ceton, in ji rahoton CBS News.

Isra'ila ta kuma bayar da tallafin bayanan sirri domin taimaka wa Amurka gano inda matuƙan suke kafin dakarun Iran su isa gare su yau.

Jirgin yaƙin F-15E da Iran ta kakkabo yana ɗaukar ma'aikata biyu ne; matuƙi da kuma jami'in sarrafa makamai.

An ce matukin jirgin Amurka 1

Jami'an Amurka sun tabbatar wa manema labarai cewa dakarun ceto na Amurka sun yi nasarar gano tare da ceto guda ɗaya daga cikin ma'aikatan. A halin yanzu, ana ci gaba da fafutukar neman ɗayan ma'aikacin.

Wannan shi ne jirgin yaƙi na farko da Amurka ta rasa a sararin samaniyar Iran tun farkon ɓallewar wannan yaƙi a ƙarshen Fabrairu, in ji rahoton CNN.

Kara karanta wannan

Ko ina ya kama da wuta: An gano ɓarnar da Iran ta yi wa Kuwait, ƙawar Amurka

Wannan babban koma-baya ne ga iƙirarin gwamnatin Trump na cewa Amurka tana da cikakken iko a sararin samaniyar Iran, kuma hakan ya sake jaddada babban haɗarin da sojojin Amurka ke fuskanta.

Martanin Trump kan kakkabo jirgin Amurka

Duk da wannan babban rashi, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa harbo jirgin ba zai canza komai dangane da tattaunawar sulhu da Amurka ke yi da Iran kan wannan yaƙi ba.

Dakarun Amurka na ci gaba da aikin ceto ma'aikatan jirgin yakinsu da Iran ta kakkabo.
Dakarun sojojin Amurka na bataliyar USMC sun isa sansanin horo na UWTCa Kudancin Isra'ila. Hoto: JACK GUEZ/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

A wata tattaunawa ta wayar tarho da gidan talabijin na NBC News, Trump ya ce:

"A'a, sam hakan ba zai shafi komai ba. Yaƙi ne ake yi, kuma muna tsaka da yaƙi."

Shugaban ya ƙi yin ƙarin bayani kan aikin ceton da ake gudanarwa, amma ya jaddada cewa yaƙin zai iya ɗaukar wasu makonni biyu zuwa uku masu zuwa.

Sai dai masana na ganin wannan yaƙi yana ƙara zama ƙaya ga Trump, duba da cewa aƙalla sojojin Amurka 13 ne suka mutu yayin da 365 suka ji rauni tun fara yaƙin.

Kasar Iran ta harbo jirgin Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun IRGC na kasar Iran sun yi nasarar harbo wani jirgin sojojin Amurka samfurin F-35 daga sama.

Kara karanta wannan

Yemen ta shiga yakin Iran gadan gadan, ta harba makami mai linzami zuwa Isra'ila

Hakan na zuwa ne bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi kan cewa zai cigaba da lalata muhimman wurare a Iran.

A daya bangaren, an samu rahotanni da suka nuna cewa an ka hari da jirgi maras matuki wata matatar mai da ke yankin Al Ahmad na Kuwait.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com