Ko Ina Ya Kama da Wuta: An Gano Ɓarnar da Iran Ta Yi wa Kuwait, Ƙawar Amurka
- Rundunar IRGC ta Iran ta kai farmaki kan matatar mai ta Mina al-Ahmadi da ke a birnin Kuwait a safiyar yau Juma'a, 3 ga Afrilu, 2026
- Kamfanin man fetur na ƙasar Kuwait (KPC) ya tabbatar da ɓallewar gobara a rukunoni da dama na matatar sakamakon harin Iran
- Gwamnatin Kuwait ta kuma tabbatar da cewa harin Iran ya lalata babbar cibiyar samar da ruwan sha da 'yan kasar suka dogara da ita
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kuwait – Yankin Tekun Fasha ya sake shiga wani babban mawuyacin hali a yau Juma'a, 3 ga Afrilu, 2026, biyo bayan jerin hare-haren da Iran ta kai kan muhimman ababen more rayuwa na ƙasar Kuwait.
Rahoto ya nuna cewa matatar mai ta Mina al-Ahmadi, ta kasance ɗaya daga cikin manyan matatun man ƙasar Kuwait.

Source: Getty Images
Iran ta farmaki matatar man Kuwait
Harin, wanda aka kai da misalin ƙarfe 8:00 na safe, ya haddasa gagarumar gobara a sassa daban-daban na matatar mai dake da ƙarfin tace ganga 346,000 a kowace rana, a cewar rahoton AP News.
Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa wannan hari na ɗaya daga cikin jerin martanin da take kai wa ƙawayen Amurka da Isra'ila a yankin.
Kamfanin man fetur na ƙasar Kuwait (KPC) ya fitar da sanarwa ta gaggawa inda ya tabbatar da cewa ƙungiyar agajin gaggawa da na kashe gobara suna bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan wutar.
Kodayake ba a bayar da rahoton asarar rai ba zuwa yanzu, KPC ya bayyana cewa, gobarar ta shafi sassa da dama na sarrafa mai a matatar.
Ana sanya ido kan ingancin iska a kewayen matatar tare da haɗin gwiwar hukumar kare muhalli (KEPA) yayin da rundunar sojin sama ta Kuwait ta kakkabo wasu daga cikin jiragen da aka harba kafin su isa manufarsu.
Yadda aka farmaki masana'antun ruwan Kuwait
Bayan harin da aka kai wa matatar mai ta Mina al-Ahmadi da sassafe, gwamnatin Kuwait ta sanar da cewa dakarun na Iran sun sake lalata wata masana'antar tace ruwan sha a wani hari na daban.
Ma'aikatar Lantarki da Ruwa ta ƙasar Kuwait ta bayyana cewa wannan hari ya yi barna sosai ga injinan da ake amfani da su wajen tace ruwan teku domin zama ruwan sha, in ji rahoton Aljazeera.
Wannan lamari ne da ya tada hankalin jama'a sosai ganin cewa kusan kashi 90 na ruwan shan da daukacin al'ummar Kuwait ke amfani da shi yana dogara ne kacokan kan waɗannan masana'antu.
Ma'aikatar ta tura ƙungiyoyin injiniyoyi na gaggawa domin duba irin asarar da aka tafka tare da ƙoƙarin tabbatar da cewa samar da ruwa bai tsaya cik ba ga gidajen jama'a yau.

Source: Getty Images
Tasirin hare-haren Iran a Gabas ta Tsakiya
Wannan shi ne hari na uku da aka kai wa matatun Kuwait a cikin makonni biyu, wanda hakan ke nuna cewa Iran ta mayar da hankali ne wajen durƙusar da tattalin arzikin ƙasashen dake marawa Amurka da Isra'ila baya.
Wadannan hare-hare sun zo ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai (Brent crude) ya yi tashin gwauron zabi, inda har ya haura $110 kan kowace ganga, wanda hakan ke nuna ƙaruwar fiye da kashi 50 tun bayan barkewar yaƙin a ƙarshen Fabrairu, 2026.
Wannan sabon salo na harin da ya shafi ruwan sha da man fetur ya jefa rayuwar miliyoyin mutane cikin haɗari a yankin.
Jiragen Amurka sun ruguzo a Kuwait
A wani labari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da rikitowar da dama daga cikin jiragen yakin kasar Amurka a Kuwait yayin da ake cigaba da yaki da Iran.
Gwamnatin Kuwait ta bayyana cewa an mika wasu daga cikin matukan asibiti domin lura da lafiyarsu bayan fadowar jirgin yakin.
A daya bangaren, an bukaci 'yan kasar Amurka da su yi taka-tsan-tsan wajen fita zuwa wurare a Bahrain yayin da Iran ke luguden wuta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


