Kasar Isra'ila Ta Aikata Mummunan Laifi, Ta Kai Farmaki Masallaci a Ranar Juma'a

Kasar Isra'ila Ta Aikata Mummunan Laifi, Ta Kai Farmaki Masallaci a Ranar Juma'a

  • Isra'ila ta farmaki musulmai jim kadan bayan sun idar sallah yau Juma'a a garin Sohmor da ke kudancin kasar Labanon
  • Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane biyu ne aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 10 suka samu raunuka
  • Wannan hari dai ya sabawa dokokin kasa da kasa, wadanda suka haramta farmakar wuraren ibada na addini da gine-ginen tarihi har a lokacin yaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lebanon - Rahotanni sun nuna cewa harin jirgi mara matuka da kasar Isra'ila ta kaddamar ya yi ajalin muatane wani masallaci jim kadan bayan musulmai sun idar da Sallah a Lebanon.

Wannan hari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, wacce ke goyon bayan Iran da kuma kasar Yahudawa watau Isra'ila.

Kara karanta wannan

Abubuwan sun cabe, an fara lalubo hanyoyin lallaba kasar Iran ta yi sulhu da Amurka

Jirgin yaki.
Jirgin yaki mara matuka da ake amfani da shi wajen lai hari Hoto: SOPA Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta kai hari masallaci a Labanon

Kafar watsa labarai ta Shafaq News ta rahoto cewa harin na Isra'ila ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, yayin da wasu 11 suka jikkata bayan kammala Sallah a masallacin.

Lamarin ya auku ne a garin Sohmor da ke kudancin kasar Labanan yau Juma'a, 3 ga watan Afrilun 2026, cewar rahoton Al-Jazeera.

Kafafen watsa labarai na cikin gida a Lebanon sun ruwaito cewa harin ya afku ne a daidai lokacin da masallata ke fitowa daga masallacin bayan kammala sallah.

Haka zalika, hukumar NNA ta Lebanon kara da cewa wani harin sararin samaniya na daban ya ruguza wata Husseiniya (wato wurin bauta na mabiya mazhabar Shi'a) a garin Srifa da ke kudancin kasar.

Harin Isra'ila ya sabawa dokar kasa da kasa

Dokokin kasa da kasa sun haramta kai hare-hare kan gine-ginen farar hula, ciki har da wuraren bauta na kowane addini.

Kara karanta wannan

An kama sojan bogi a Jos yayin da ake kashe kashe a Filato

Yarjejeniyar Geneva ta shekarar 1977 ta tilasta wa bangarorin da ke yaki da su kare kadarorin farar hula, sannan ta haramta mayar da su wuraren kai hari.

Haka kuma, dokar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2347 (na shekarar 2017), ta bayyana lalata wuraren addini da na tarihi a matsayin laifin yaki (war crime), wanda hakan na bukatar hukunci ga wadanda suka aikata.

Netanyahu.
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Alkaluman wadanda hare-hare suka shafa

Isra'ila ta ci gaba da tsananta kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar Labanan, musamman a yankunan kudanci da kuma unguwannin karkashin birnin Beirut.

Kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta sanar, ya zuwa yanzu akalla mutane 1,345 ne aka kashe yayin da was mutane 4,040 sun jikkata.

Cikin wadanda abin ya shafa har da yara kanana 125 da mata 88, sannan ma'aikatan lafiya sama da 150 ne suka rasa rayukansu a cikin wannan rikici.

Iran ta jikkata fiye da Yahudawa 100

A wani labarin, kun ji cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hare-hare ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila.

Kara karanta wannan

Yahudawa sun ga ta kansu da makamin Iran ya afka masu a babban birnin Isra'ila

Ma'aikatar lafiyar Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kai mutane 148 da suka ji rauni zuwa asibitoci sakamakon hare-haren Iran.

Ta ce tun farkon fara yaƙin da Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, an kwantar da mutane 6,594 a asibitoci, inda a halin yanzu mutane 124 ke ci gaba da jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262