Iran Ta Lissafo Wuraren da za Ta Kai wa Hari idan Amurka ba Ta Shiga Taitayinta ba
- Iran ta ce za ta mayar da martani idan Amurka ta kai sake hari kan tashoshin lantarki da ke sassan kasarta
- Ta yi barazanar kai hari ga kamfanonin makamashi da sadarwa masu hannun jarin Amurka a Gabas ta Tsakiya
- Jami’an sojin Iran sun ce sun shirya daukar matakin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya matukar Amurka ta ci gaba da kai mata hari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Iran – Iran ta yi kakkausar gargadi ga Amurka, inda ta bayyana cewa za ta dauki matakin ramuwar gayya idan har ta ci gaba da barazanar kai hari kan tashoshin lantarki na kasar.
Mai magana da yawun rundunar sojin Iran, Ebrahim Zolfaghari, ya bayyana cewa Tehran za ta mayar da martani kai tsaye idan aka kai hari kan muhimman ababen more rayuwa na kasar.

Kara karanta wannan
Bayan haura wata 1 ana yaki, Shugaba Macron ya fada wa Amurka gaskiya kan shirin nukiliyar Iran

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa Zolfaghari ya kara da cewa duk wani hari daga Amurka zai jawo martani mai tsauri daga Iran, wanda zai iya shafar muhimman tsare-tsare a yankin.
Iran ta tura sakon gargadi ga Amurka
Time Magazine ta ruwaito cewa Iran ta e za ta kai hari a kan manyan kamfanonin sadarwa da ke da alaƙa da Amurka ga duk kisan da aka kuma yi a ƙasar.
Ebrahim Zolfaghari, ya bayyana cewa:
"Idan Amurka ta ci gaba da barazanar kai hari kan tashoshin lantarki na Iran, za mu dauki matakin da ya dace domin kare muradunmu.”
Haka kuma, jami’in ya yi gargadin cewa Iran za ta kai hari ga cibiyoyin makamashi da kuma kamfanonin sadarwa a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman wadanda ke da masu zuba jari daga Amurka.
Ya ce:
“Za mu kai hari ga cibiyoyin makamashi da kamfanonin fasaha da sadarwa da ke da alaka da Amurka a yankin.”
Kasar Iran ta gargadi wasu ma'aikata
IRGC ta kara da cewa ma’aikatan wadannan kamfanoni su gaggauta barin wuraren aikinsu nan take.
Ta shawarci mazauna dukkannin kasashen yankin aka bukace su da su fice daga duk wata cibiyar da ke cikin tazarar kilomita daya daga wadannan wurare.
Wannan sanarwa na nuna cewa wuraren da IRGC za ta iya kai hari sun hada da muhimman ababen more rayuwa na wadannan kamfanonin fasaha a fadin Gabas ta Tsakiya, amma ba lallai ba ne su hada da cibiyoyin da ke cikin Amurka.

Source: Getty Images
Kamfanonin da aka lissafa sun hada da Cisco; HP; Intel; Oracle; Microsoft; Apple; Google; Meta; IBM; Dell; Palantir; Nvidia; JPMorgan Chase; Tesla; General Electric; da kuma Boeing.
Haka kuma, an ambaci wasu kamfanoni biyu da hedikwatarsu ke UAE: G42, wani kamfanin fasahar basirar wucin gadi da ke Abu Dhabi, da kuma Spire Solutions, kamfanin tsaron yanar gizo da ke Dubai.
Iran ta kakkabo jirgin Amurka
A baya, mun wallafa cewa rahotanni daga Tehran sun nuna cewa dakarun Iran sun yi nasarar harbo wani jirgin sojojin Amurka samfurin F-35 daga sama.
Hakan na zuwa ne bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi kan cewa zai cigaba da lalata muhimman wurare a Iran idan ba ta amince da sulhu ba.
A daya bangaren, an samu rahotanni da suka nuna cewa an ka hari da jirgi maras matuki wata matatar mai da ke yankin Al Ahmad na Kuwait yayin da ake ci gaba da yakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

