Abubuwan Sun Cabe, An Fara Lalubo Hanyoyin Lallaba Kasar Iran Ta Yi Sulhu da Amurka

Abubuwan Sun Cabe, An Fara Lalubo Hanyoyin Lallaba Kasar Iran Ta Yi Sulhu da Amurka

  • Jamus ta fara bin hanyoyin da za a lallaba kasar Musulunci ta Iran ta dawo teburin tattaunawa domin kawo karshen yakin Amurka/Isra'ila
  • Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke ci gaba da musayar wuta da Amurka/Isra'ila, yakin da ya shafe sama da wata guda
  • Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta tabbatar da cewa China za ta iya amfani da alakarta da Iran wajen kawo karshen wannan rikici

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Germany - A wani mataki na diplomasiyya da nufin kwantar da tarzoma a yankin Gabas ta Tsakiya, gwamnatin Jamus ta bukaci kasar China da ta yi amfani da dukkan tasirinta don ganin an koma teburin tattaunawa da Iran.

Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar yakin da ya barke tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila na iya daukar dogon lokacin da ba a yi tsammani ba.

Kara karanta wannan

Bayan haura wata 1 ana yaki, Shugaba Macron ya fada wa Amurka gaskiya kan shirin nukiliyar Iran

Shugaban China.
Shugaban kasar China, Xi Jinping a wurin taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jamus ta tura bukata ga China

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus ta tabbatar da cewa babban jami'inta na diflomasiyya, Johann Wadephul, ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar China, Wangi Yi.

Babban makasudin wannan kiran waya shi ne nazarin halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da kuma nemo hanyoyin da za a bi don kawo karshen rikicin cikin gaggawa.

Bangarorin biyu sun jaddada fatansu na ganin an samu maslaha wadda za ta amfani dukkan kasashen da abin ya shafa.

Batun mashigar ruwa ta Hormuz

Wani muhimmin bangare na tattaunawar ya mayar da hankali ne kan mashigar ruwa ta Hormuz, wadda take daya daga cikin hanyoyin sufurin mai mafi muhimmanci a duniya.

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bayyana a wani sako da ta fitar cewa, dukkanin kasashen biyu (Jamus da China) suna da muradin ganin an samu 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa.

Kara karanta wannan

2027: Jerin ministoci da manyan jami’an gwamnatin Tinubu 7 da suka yi murabus don takara

Sun amince cewa, a karkashin dokokin kasa da kasa, bai kamata kowace kasa ta yi ikirarin mallakar hanyoyin ruwa na duniya ko sanya haraji ga jiragen da ke ratsawa ta cikinsu ba.

Wannan matsayi na Jamus da China ya zo ne a matsayin martani ga fargabar cewa Iran na iya toshe mashigar ko kuma sanya tsauraran sharudda ga jiragen kasashen yamma.

Khamenei.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Rawar da China za ta iya takawa

Jamus ta bayyana karara cewa China tana da wani matsayi na musamman wanda zai iya taimakawa wajen shawo kan lamarin, kamar yadda NBC News ta rahoto.

Sakamakon alakar ciniki mai karfi da ke tsakaninsu, China tana da "karfin iko" da za ta iya amfani da shi don matsa wa Iran lamba ta yadda za ta amince da hanyar tattaunawa maimakon yin amfani da karfin soja.

Bugu da kari, Jamus na fatan cewa sa baki daga China zai kawo karshen tashe-tashen hankula da ake yi da kasashen yankin Gulf, wadanda suke fuskantar barazana daga dakarun dake samun goyon bayan Iran.

Iran ta samu sakon bukatar tsagaita wuta

An ji cewa Iran ta tabbatar da cewa ta karbi sakon bukatar tsagaita wuta a yakin da kasar ta shafe sama da wata guda tana yi da Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Da alama yaki ya zo karshe, kasar Musulunci ta Iran ta karbi sako daga Amurka

Amma duk da haka, Iran ta sake jaddada cewa hakan ba yana nufin ta hau teburin tattaunawar diplomasiyya da Amurka ko Isra'ila ba ne.

Tun farko dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya musanta rade-radin cewa sun hau teburin tattaunawa da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262