Yaki Ya Canza Salo, Kasar Iran Ta Bullo da Dabarun Ruguza Shirin Sojojin Amurka
- Rundunar sojojin Iran sun fara shirye-shiryen tunkarar sojojin da Amurka ta yi barazanar turowa cikin Jamhuriyar musulunci
- Kwamandan sojojin Iran, Amir Hatami ya umarci dakarun kasar su zage damtse wajen sanya ido da bibiyar duk wani motsi da ba su aminta da shi ba
- Ya kuma ba da umarnin fara shirin ko ta kwana domin tunkarar sojojin Amurka idan sun shigo kasar da wata manufa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawo shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Dakarun sojojin kasar Musulunci ta Iran sun bayyana cewa za su kara dagewa cikin matukar kula da dabaru wajen sanya ido kan masu taimakawa Amurka da Isra'ila
Babban kwamandan rundunar sojin ƙasar Iran, Amir Hatami ne ya bayyana hakan yayin da yakin kasar da Amurka/Isra'ila ke shirin shiga wani mataki a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Sojojin Iran sun kara tashi tsaye
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa kwamandan ya umarci da su sanya ido kan duk wani motsi na Amurka da Isra’ila “kowace dakika”, da nufin tunkarar duk wani yiwuwar hari na ƙasa da za a iya kaiwa ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa yana dab da karkare hare-haren da ake kai wa Iran.
Trump ya kuma nuna alamun cewa da yiwuwar ya tura dakarun sojojin kasa su shiga cikin Iran domin kwace wasu muhimman wurare ciki har da kwato sinadarin Uranium.
Wannan ya sa sojojin Iran da mayakan da ke goya masu baya suka tashi tsaye da nufin tunkarar duk wata barazana da ka iya biyo baya idan sojojin Amurka sun shiga kasar.
Dabarun da sojojin Iran suka bullo da su
Babbar rundunar sojojin Iran ta sanar da cewa jami'anta za su kara sanya ido da matukar kula domin dakile duk wani yunkurin makiyan kasar, cewa rahoton AI Monitor.
A cikin wani bidiyo da hukumomin Iran suka fitar, an nuno Shugaban Rundunar Sojin ƙasar, Amir Hatami, lokacin da yake ganawa da sauran shugabannin sojoji.
“Idan maƙiyi ya yi ƙoƙarin ƙaddamar da ayyukan soja ta ƙasa, kada mutum ko guda ya tsira,” in ji Hatami.

Kara karanta wannan
Shugaba Pezeshkian ya gano masu goyon bayan Iran a yaki da Amurka, ya aika masu sako

Source: Getty Images
Shugaban sojojin ya kara da cewa wannan aiki yana da matukar muhimmanci a kokarin da Iran ke yi na kare kanta daga duk wata barazana da za ta taso daga Amurka ko Isra'ila.
Ya kara da cewa:
"Yana da muhimmanci a sa ido kan duk wani motsi da ayyukan maƙiya da matuƙar kula da kwarewa a kowane lokaci, sannan a aiwatar da tsare-tsare na tunkarar duk wasu hanyoyin da maƙiyi zai iya bi wajen kai hari.”
Sojojin Iran sun kara harba makami
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da hare-hare kan muhimman wurare na Amurka da Isra'ila.
Rundunar IRGC ta farmaki wasu sansanonin sojoji na Amurka yayin da ta harba jerin makamai masu linzami a rukuni na 83 na hare-haren ramuwar gayyar da take kai wa.
Daga cikin wuraren da aka farmaka akwai rumbunan adana mai a Ashdod, wurin zama na ma'aikatan soja a Modi'in, da kuma cibiyar musayar bayanan sirri ta sojin Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
