Yahudawa Sun Ga Ta Kansu da Makamin Iran Ya Afka Masu a Babban Birnin Isra'ila

Yahudawa Sun Ga Ta Kansu da Makamin Iran Ya Afka Masu a Babban Birnin Isra'ila

  • Hukumomin kasar Yahudawa watau Isra'ila sun bayyana wasu daga cikin barnar da hare-haren Iran suka yi wa mutane a kusa da Tel Aviv
  • Ma'aikatan lafiya da ke bada agajin gaggawa a Isra'ila sun ce akalla mutane 14 suka samu rauni a harin makamin Iran a yankin Bnei Brak
  • Daga cikin wadanda suka samu rauni har da yarinya yar shekara 11 kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta bayyana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila yayin da yakin da ya barke tsakanin kasashen ke kara kamari a Gabas ta Tsakiya.

Hukumomin kasar Isra'ila sun tabbatar da cewa harin da Iran ta kai yau Laraba a yankin Bnei Brak, kusa da birnin Tel Aviv, ya yi barna tare da jikkata mutane da dama.

Kara karanta wannan

Mamaki ya kama Isra'ila da makaman Iran suka lalata dakunan kariyarta

Netanyahu.
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu a wurin da Iran ta kai hari Hoto: Alexi Rocenfeld
Source: Getty Images

Iran ta jikkata Yahudawan Isra'ila 14

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa hukumomin da ke da alhakin kai dauki da ba da agajin gaggawa na Isra'ila ce makamin da Iran ta harbo ya raunata mutane 14 a kusa da birnin Tel Aviv.

Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga wata na biyu da fara musayar wuta tsakanin Iran da hadin guiwar Amurka da Isra'ila, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin tashin hankali.

Hukumomin agajin gaggawa na Isra'ila sun bayyana cewa mutanen da suka raunata a kusa da birnin Tel Aviv sun hada da wata yarinya ’yar shekara 11.

Kananan yara sun jikkata a harin Iran

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta bayyana cewa ta duba mutane 14 da suka raunata a yankin Bnei Brak tare da kwashe su zuwa asibiti.

Ta kara da cewa yarinyar da lamarin ya shafa na cikin wani yanayi mai tsanani sakamakon raunuka da gutsuren bama-bamai suka yi mata.

Kara karanta wannan

Amurka ta ci karo da cikas, Iran ta illata ta a yakinta da kasar Isra'ila

Hukumar ta ce akwai wani yaro dan shekara 13 da kuma wata mace mai shekaru 36 wadanda suma suka sami raunukan gutsuren bam.

Sai dai ta tabbatar da cewa ana ba su kulawar da ya dace kuma yanayinsu ba shi da muni sosai, yayin da sauran mutane 11 da suka samu raunuka masu sauki.

Harin Iran.
Yadda ake harba makamai masu linzami a yakin Iran da Isra'ila Hoto: Anadolu
Source: Twitter

Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa wadannan raunuka sun afku ne sakamakon harin makami mai linzami da kasar Iran ta kaddamar.

Babu wani rahoto da ke nuna cewa an rasa rayukan a sababbin hare-haren da Iran ta kai birnin Tel Aviv, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Iran ta harba makamai sama da 300

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar IRGC ta Iran ta sanar da harba makamai masu linzami da suka haura 100 tare da rokoki 300 kan sansanonin sojin Amurka da Isra'ila.

IRGC ta tabbatar da cewa hare-haren sun daki muhimman wurare, ciki har da wani katafaren ginin sojin Amurka dake ƙasar Bahrain.

Rundunar ta yi gargaɗi cewa waɗannan ayyukan soji za su ci gaba da gudana cikin "cikakken ƙarfi da izza" muddin ba a daina kai wa shugabannin Iran hari ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262