Trump Ya Gindaya Sharudan Tsagaita Wuta, Ya Fadi Rokon da Iran Ta Yi Masa
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da yunkurin tsagaita wuta da Iran ta nema a yi a yaƙin da ake yi
- Trump ya ce Shugaban Iran yana neman tsagaita wuta, duk da sabanin kalamansa kan dakatar da yakin ko kara tsananta shi
- Iran ta ci gaba da kai hare-hare a yankin Tekun Fasha, yayin da farashin mai ya tashi sakamakon rikicin da ya shafi mashigar Hormuz
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa shugaban Iran yana neman tsagaita wuta.
Wannan na zuwa ne yayin da ake kai hare-hare, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da wanda yake nufi ba game da neman a tattauna.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana haka ne a yau Laraba 1 ga watan Afrilun shekarar 2026 a shafin sada zumunta na Truth Social.
A cikin rubutunsa, ya ce:
“Sabon shugaban gwamnatin Iran, wanda bai da tsattsauran ra’ayi sosai kuma ya fi wayo fiye da wadanda suka gabace shi, yanzu ya roki Amurka ta tsagaita wuta! Za mu yi la’akari ne kawai idan mashigar Hormuz ta bude, ta zama kyauta kuma babu wani cikas. Har sai hakan ta faru, muna ci gaba da ragargazar Iran gaba daya ko kuma, kamar yadda suke fada, mayar da su zamanin baya."
Trump ya kuma nuna sabani a kalamansa kan ko zai kawo karshen yaki ko kuma ya kara tsananta shi, cewar rahoton Fox News.
Gargadin da Trump ya yi kan mashigar Hormuz
A yau Laraba, 1 ga watan Afrilun 2026, Trump ya yi gargadi mai tsauri cewa idan Iran ba ta bude mashigar Hormuz ba, Amurka za ta kai mata hari mai tsanani.
Wannan hanya ce mai muhimmanci wajen jigilar mai a duniya, kuma rikicin ya jawo tashin farashin mai sosai.
Duk da ikirarin tsagaita wuta, Iran ta ci gaba da kai hare-hare a kasashen yankin Tekun Fasha wanda ke sanya shakku ko maganar Trump gaskiya ce
Har ila yau, Amurka na kara tura sojoji yankin, lamarin da ke nuna yiwuwar kara fadada rikicin zuwa yakin kasa duk da asarar rayuka da dukiyoyi da ake yi.

Source: Facebook
Martanin Ministan harkokin wajen Iran
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa kasarsu ba za ta amince da barazana ba, yana mai cewa Iran ba ta sanya wa kanta wa’adin kare kanta daga hare-hare ba.
Rahotanni sun nuna cewa jiragen ruwa masu dauke da mai sun fuskanci hare-hare a kusa da Qatar da Dubai da sauran ƙasashen yankin, cewar rahoton PBS News.
Sai dai wasu kasashe sun dakile makamai masu linzami da jirage marasa matuki daga Iran ba tare da samun asarar rayuka ba wanda ke nuna cewa suna fama da hare-haren a yankin.
A lokaci guda, hare-haren sama sun lalata wasu gine-gine a Tehran, ciki har da wuraren tarihi, yayin da Isra’ila ta kai hari Lebanon inda aka kashe mutane da dama. Rikicin ya haddasa mutuwar dubban mutane da kuma gudun hijira a yankin.
Trump ya gargadi Iran game da tattauanawa
Mun ba ku labarin cewa, Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargadi mai tsauri ga hukumomi a Iran kan bijirewa sharudan zaman lafiya.
Ya yi barazanar cewa idan Iran ta ki amincewa da wadannan sharuda, matakin Amurka zai tsananta kuma 'ba zai yi kyau ba' saboda matakin da za su dauka.
Trump ya kuma soki NATO yana cewa kasashen kungiyar ba su taimaka ba a yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin dubban al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


