Kwan Gaba Kwan Bayan Donald Trump a Yakin Amurka da Iran
Birnin Washington, Amurka - Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kalamai masu cin karo da juna kan yakin da kasarsa ke yi da Iran.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Trump da takwaransa na Isra'ila, Benjamin Netanyahu, sun ƙaddamar da gagarumin harin soja kan Iran, inda suka kashe jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei da mutane da dama ciki har da mata da yara.

Source: Getty Images
Amurka da Isra'ila sun farmaki Iran
Tashar CNN ta ce Amurka da Isra'ila sun kai hari Iran tare da kashe jagoran addini kasar, Ali Khamenei, a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
A lokaci guda kuma, Amurka da Isra'ila sun ci gaba da jefa bama-bamai, ciki har da kashe yara mata ƴan makaranta sama da 150 a wata makarantar mata zalla a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Tufka da warwarar Trump a yakin Iran
Legit Hausa ta zakulo wasu kalamai da shugaban na Amurka ya yi waɗanda suka saɓa wa ayyukansa, ko abin da ya faru, ko kuma abin da ya kasa bayar da hujjarsa.
Ga jerinsu nan a ƙasa:
1. Iƙirarin Trump kan diflomasiyya
"Abin da na fi so shi ne a magance wannan matsalar ta hanyar diplomasiyya. Dan lokaci kaɗan da ya wuce, dakarun sojin Amurka suka fara manyan ayyukan yaƙi a Iran."
Trump ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na Truth Social
Trump ya ce yana ƙoƙarin magance matsalar ne ta hanyar diflomasiyya, amma sai ya ƙaddamar da yaƙi a tsakiyar tattaunawa da Iran.
2. Iƙirarin Trump na yin nasara a yaƙin
Tashar Aljazeera ta ce Trump ya yi ikirarin yin nasara tun a farkon fara yakin.
"Ku sani, ba a cika son faɗa da wuri cewa mun yi nasara ba. Mun yi nasara, amma a sa’ar farko komai ya ƙare."

Kara karanta wannan
Wuya ta yi wuya: Isra'ila ta dakatar da kai hare hare kan kasar Iran, an ji dalili
- Donald Trump
Shugaban na Amurka ya yi iƙirarin cewa ya yi nasara a yaƙin a harin farko, amma yaƙin ya ci gaba da gudana kusan wata guda bayan hakan.
3. Kalaman Trump kan mashigar Hormuz
Donald Trump ya nemi taimakon kasashe domin bude mashigar Hormuz wadda Iran ta kulle.
Tashar PBS News ta ambato shugaban na Amurka na cewa:
"Muna karfafa gwiwar kasashen da tattalin arzikinsu ya dogara da mashigar Hormuz fiye da mu, muna samun kasa da kaso 1 na man mu daga mashigar, wasu kasashen suna samun fiye da haka."
"Japan tana samun kaso 95, China tana samun kaso 90, wasu daga cikin kasashen Turai na samu da yawa, Koriya ta Kudu tana samun kaso 35. Saboda haka muna son su zo taimaka mana wajen bude mashigar."
Sai dai kuma daga baya Trump ya ce baya bukatar taimakon wata kasa wajen bude mashigar Hormuz.
"Ba mu bukatar kowa, mu ne kasa mafi karfi a duniya, muna da sojojin da babu irinsu a duniya, ba mu bukatarsu. Amma kuma ina yin hakan ne domin na ga martanin da za su yi."
- Donald Trump

Source: Getty Images
4. Barazanar hari kan tashoshin lantarkin Iran
Trump ya yi barazanar kai hari kan tashoshin lantarkin Iran, inda ya ba mahukuntan kasar wa'adin sa'o'i 48 kan su bude mashigar Hormuz, ko kuma ya yi abin da ya ce zai yi.
A wani rubutu a shafinsa na Truth Social, Trump ya rubuta cewa:
"Idan har Iran ba ta bude mashigar Hormuz gaba daya ba, kuma ba tare da barazana ba, nan da sa'o'i 48 daga daidai wannan lokacin, Amurka za ta farmaki tare da lalata dukkan tashoshinsu na samar da wutar lantarki daban-daban, za mu fara da mafi girmansu tukuna."
- Donald Trump
Sai dai, daga baya Trump ya janye wannan wa'adin da ya ba da inda ya kara tsawaita shi zuwa 6 ga watan Afirilun 2026.
5. Ikirarin kin yin yarjejeniya da Iran
Trump ya bayyana a shafinsa na Truth Social cewa ba zai cimma wata yarjejeniya da Iran ba har sai ta mika wuya.

Kara karanta wannan
Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila
"Babu wata yarjejeniya da za a yi da Iran sai dai idan sun mika wuya ba tare da wani sharadi ba! Bayan hakan, da kuma zaɓar Jagora (ko jagorori) na gari kuma karbabbu, mu, tare da da dama daga cikin ƙawayenmu da abokan haɗin gwiwarmu masu ban mamaki da jarumta, za mu yi aiki dare da rana don dawo da Iran daga gaɓar rugujewa, tare da sanya tattalin arziƙinta ya zama mafi girma, mafi kyau, kuma mafi ƙarfi fiye da kowane lokaci a baya."
- Donald Trump
Sai dai daga baya a wani rubuta a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce sun tattauna da Iran tare da samun mafita kan rikicin da ake yi.
"Ina farin sanar da cewa Amurka da kasar Iran sun gudanar da tattaunawa mai kyau a cikin kwanaki biyu da suka gabata, dangane da samun mafita kan dukkanin rikicin da ke tsakaninmu a Gabas ta Tsakiya."
- Donald Trump
Amurka ta fadi kasashen da ke taimakon Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi tsokaci kan kasashen da ke taimakon Iran a yakin da ake yi.
Hegseth ya bayyana cewa sojojin Amurka sun san cikakkiyar rawar da China da Rasha ke takawa wajen taimakawa Iran a yakin da ake yi.
Minstan tsaron na Amurka ya ce suna daukar matakai na rage tasirin wannan taimako tare da tinkarar duk wata barazana kai tsaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

