Rundunar IRGC Ta Yi wa Isra'ila Barna a Sababbin Hare Haren Makami Mai Linzami
- Makamai masu linzami na Iran sun daki wani babban gini a Bnei Brak inda aka kwashe yara da mata zuwa asibiti bayan sun ji rauni
- Hukumar MDA ta tabbatar da jikkatar mutane tara a sassan Tel Aviv da Petah Tikva sakamakon barbashin makaman da suka tarwatse
- Dakarun sojin Isra'ila sun gano ƙarin makamai daga Iran dake tunkarar sassan kudancin ƙasar bayan harin da aka kai tsakiyar ƙasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Isra'ila - Babbar gobara ta tashi a Bnei Brak bayan wani makami mai linzami da Iran ta harba ya faɗa kai tsaye cikin birnin a safiyar Laraba.
Dakarun kashe gobara da na ceto sun garzaya yankin domin shawo kan wutar dake ƙoƙarin yaɗuwa zuwa gidajen mutane dake maƙwabtaka da inda harin ya faru.

Source: Getty Images
Iran ta yi wa Isra'ila barna a sabon hari
A halin yanzu, ƙungiyar agaji ta MDA tana ba waɗanda suka ji raunuka kulawar gaggawa a Bnei Brak, Petah Tikva, da kuma Tel Aviv, a cewar rahoton Aljazeera.
A birnin Bnei Brak, an bayar da rahoton cewa wata uwa da yaranta biyu sun ji rauni sakamakon barbashin makami da ya samesu, yayin da wata matar ta ji rauni daga gutsuren gilashi.
Wani ma'aikacin MDA, Yehuda Shoshana, ya bayyana cewa sun dauke jariri ɗan wata shida, yaro ɗan shekara shida da rabi, da kuma wata mace ƴar kusan shekara 40 zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.
Makaman Iran sun fada wurare 4 a Isra'ila
Kafar yaɗa labarai ta Israel National ta rahoto cewa akwai wurare guda huɗu da makaman Iran ɗin suka faɗa a tsakiyar Isra'ila: biyu a Bnei Brak, ɗaya a Holon, sai kuma guda ɗaya a Petah Tikva.
Harin ya lalata sashen saman wani ginin zama a Bnei Brak, yayin da gobarar ta tashi a wani fili dake Holon da Petah Tikva sakamakon harin.
An kuma samu rahotanni na ƙarin makamai da aka harba daga Iran zuwa yankunan arewa da kudancin Isra'ila jim kaɗan bayan harin na tsakiyar ƙasar yau.

Source: Getty Images
Gargaɗin shigowar jirage marasa matuka
Duk da cewa wasu makaman na baya-bayan nan sun faɗa ne a sarari ba tare da janyo raunuka ba, ƙararrawar gargaɗi ta karaɗe sassan Isra'ila baki ɗaya.
Haka kuma, an bayar da gargaɗi game da shigowar jirage marasa matuƙa a yankin Western Galilee dake arewacin Isra'ila, lamarin da ya jefa mutane cikin fargaba.
Wannan yaƙin na yau Laraba ana ganinsa a matsayin martani mai tsanani da Iran take yi wa Isra'ila biyo bayan hare-haren da aka kai mata a kwanakin baya.
Amurka da Isra'ila sun sake tafka asara
A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun sojojin kasar Iran sun yi ikirarin kakkabo jirgin leken asiri kirar MQ-9 Reaper, wanda darajarsa ta kai Dala miliyan 30.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin MQ-9 Reaper na daga cikin manyan jiragen leken asiri da ake amfani da su wajen kai hare-hare da tattara bayanai.
Sojojin Iran sun ce wannan jirgi shi ne na 146 da suka harbo tun bayan barkewar yaki tsakanin Jamhuriyar Musulunci da kasashen Amurka da Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


