Trump Ya Gamu da Matsala a Amurka, Kotu Ta Tsayar da Aikin $400m Ana Yakin Iran
- Alƙali Richard Leon ya ba da umarnin dakatar da ginin katafaren zauren taro na dalar Amurka miliyan 400 a fadar White House dake Washington DC
- Kotu ta bayyana cewa Shugaba Donald Trump ba shi ne 'mai gidan White House' ba, don haka dole ne ya nemi izinin majalisa don yin aiki a fadar
- Shugaba Trump ya bayyana masu adawa da ginin a matsayin "mahaukata" yayin da gwamnatinsa ta sanar da daukaka kara kan hukuncin na Leon
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Wani alƙalin kotun tarayya a Amurka ya dakatar da Shugaba Donald Trump daga ci gaba da kowane irin aiki kan katafaren zauren taro na dala miliyan 400 da ake shirin gina wa a tsohon filin fadar White House.
A hukuncin da ya yanke ranar Talata, Alƙali Richard Leon, ya bayyana cewa shugaban Amurka amintaccen mai kula da fadar ne kawai, amma ba shi ne mamallakin gidan ba.

Source: Getty Images
Kotu ta dakatar da babban shirin Trump
Kafar watsa labarai ta CNN ta ruwaito Mai shari'a Leon ya sanar da cewa:
"Shugaban Amurka shine mai kula da fadar White House ga iyalai masu zuwa nan gaba. To amma, ba shi ne mamallakin gidan ba!"
Babban dalilin da ya sa Mai shari'a Leon ya dakatar da aikin shi ne yadda Trump ya gaza samun amincewar ƴan majalisa kafin fara wannan ƙasaitaccen aiki, wanda dokar tarayya ta tanada.
Alƙalin ya jaddada cewa:
"Muddin majalisa ba ta albarkaci wannan aiki ta hanyar doka ba, to dole ne a dakatar da ginin!"
An ɗage aiwatar da wannan hukunci na tsawon makonni biyu domin bai wa gwamnati damar ɗaukaka ƙara, amma alƙalin ya yi gargaɗin cewa, za a rushe duk wani ginin da aka yi a tsakanin wannan lokacin.
Matsayin ginin da aka dakatar ga Trump
Shugaba Trump, wanda tsohon ɗan kasuwar gine-gine ne, ya nuna sha'awar sa sosai kan wannan aiki, inda yake sa ido tun daga kan fasalin zane har zuwa zaɓen kayan aikin da za a yi amfani da su.
An kiyasta cewa katafaren zauren yana da girman ƙafa 89,000, wanda hakan ya nunka babban ginin fadar White House mai girman ƙafa 55,000 kawai.
Trump ya bayyana wa manema labarai cewa:
"Ina fuskantar yaƙe-yaƙe da sauran abubuwa, amma wannan aikin yana da matuƙar muhimmanci domin zai kasance tare da mu na tsawon lokaci. Ina jin zai zama zauren taro mafi girma a duniya."

Source: Twitter
Trump ya caccaki masu sukar ginin
Jim kaɗan bayan hukuncin kotun, Shugaba Trump ya yi martani a shafinsa na Truth Social, inda ya soki ƙungiyar masu fafutukar kare gine-ginen tarihi waɗanda suka shigar da ƙarar.
Ya kira ƙungiyar da sunan "Kungiyar mahaukata," inda ya bayyana cewa wannan ƙara da aka shigar ba ta da wata ma'ana a wajensa.
Trump ya sha alƙawarin cewa za a kammala wannan aiki a lokacin bazara na shekarar 2028, watanni kaɗan kafin ya bar ofis, yana mai jaddada cewa bai kamata a saka wa aikin ido ba.
An fara rushe wani bangare na White House
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya bada umarnin rushe bangaren Gabashin fadar shugaban kasar Amurkan don gina katafaren dakin taro.
Tun ma kafin a fara aikin, Donald Trump ya shaida wa duniya cewa da kudin aljihunsu da na 'yan gudunmawa ne za a gina dakin taron.
An dai ga manyan injinan gine-gine suna rusa bangon ginin 'East Wing', bangaren da aka saba amfani da shi a matsayin ofishin uwargidar shugaban kasa, dakin kallo, da kuma kofar karbar baki daga kasashen waje.
Asali: Legit.ng


