Trump Ya Fusata da Wasu Ƙasashe Suka Fara Juya Masa Baya a Yaki da Iran

Trump Ya Fusata da Wasu Ƙasashe Suka Fara Juya Masa Baya a Yaki da Iran

  • Shugaba Donald Trump ya fusata kan abin da wasu ƙasashe daga Nahiyar Turai suka yi yayin yaki da Iran
  • Trump ya soki Faransa saboda hana jiragen Amurka masu ɗauke da kayan soja zuwa Isra’ila wucewa ta sararin samanta yayin rikicin Iran
  • Trump ya kuma soki Birtaniya da wasu ƙasashe, yana gargadin cewa Amurka ba za ta ci gaba da kare su ba idan ba su nuna jajircewa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya soki ƙasar Faransa kan abin da ya kira rashin nuna masa goyon baya.

Trump ya bayyana cewa kasar ba ta taimaka ba a yaƙin Iran bayan hana jiragen Amurka wucewa.

Trump ya caccaki wasu ƙasashen Turai
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka yayin kamfe a New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Trump ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa wanda Al Jazeera ta gano a yau Talata 31 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara maganar laftawa Larabawa kudin diyya kan yakin Trump da Iran

Trump ya dura kan Faransa game da yakin Iran

Ya ce Faransa ta hana jirage masu ɗauke da kayan soja zuwa Isra’ila ratsa sararin samaniyarta wanda haka ya fusata shugaban duba da yakin da ake ciki.

Ya ƙara da cewa Amurka za ta tuna da wannan mataki, yana mai zargin Faransa da rashin taimako kan abin da ya kira kawar da “makashin Iran”.

Majiyoyi sun shaida cewa lamarin ya faru ne a ƙarshen mako, kuma shi ne karo na farko da Faransa ta hana irin wannan izini tun fara farmakin Iran.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Italiya ta ƙi amincewa jiragen yaƙin Amurka su sauka a wani sansani a Sicily, yayin da Sifaniya ta rufe sararinta.

Ministar tsaron Sifaniya ta ce tun farko an bayyana cewa ba za a amince da amfani da sansanonin ƙasar ko sararin samanta ba a yaƙin Iran.

Faransa da Birtaniya sun yi wa Trump tsiya a yakinsa da Iran
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron yayin jawabi a Paris. Hoto: Emmanuel Macron.
Source: Getty Images

Kawayen Amurka da Donald Trump ya caccaka

Trump ya kuma soki wasu ƙawayen Amurka ciki har da Birtaniya, yana cewa su na fama da ƙarancin man jirgin sama saboda matsalar mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Trump zai janye yaki da Iran ba tare da cika wani burinsa ba

Ya shawarce su da su sayi mai daga Amurka kuma su ƙara jajircewa wajen kare kansu, maimakon dogaro da Amurka kawai, cewar New York Times.

Har ila yau, ya bukaci hadin kai daga gare su domin ganin an sauya jagoranci a Jamhuriyar Musulunci ta Iran duba da halin da ake ciki.

A ƙarshe, Trump ya yi gargadi cewa Amurka ba za ta ci gaba da taimaka wa ƙawayenta ba idan su ma ba su tsaya mata ba a lokutan rikici.

Karin bayani na tafe....

Trump zai janye yaki da Iran

A baya, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya fara maganar janyewa daga yaki da Iran ta bayan fage bawan shafe wata guda ana gwabzawa.

Wani rahoto da aka samu daga fadar White House ya nuna cewa Donald Trump ya ce zai janye daga yakin ko ba a bude mashigar Hormuz ba.

A daya bangaren kuma, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa bai san lokacin da yakin zai kare ba a halin yanzu wanda ya jawo asarar rayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.