Amurka Ta Fara Maganar Laftawa Larabawa Kudin Diyya kan Yakin Trump da Iran

Amurka Ta Fara Maganar Laftawa Larabawa Kudin Diyya kan Yakin Trump da Iran

  • Fadar White House ta fara magana kan yiwuwar sanya kasashen Larabawa su biya Amurka kudin da ta kashe a yaki da kasar Iran
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ya fara nuna alamun janyewa daga yakin ko ba a bude mashigar Hormuz ba
  • Mai magana da yawun fadar White House, Karoline Leavitt ce ta bayyana haka, inda ta ce shugaba Trump ba zai ki son hakan ta faru ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka Donald Trump na da sha’awar kira ga ƙasashen Larabawa su taimaka wajen ɗaukar nauyin kuɗin yaƙin Iran.

Kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, ta bayyana a ranar Litinin, inda ta ƙara da cewa tattaunawa da Tehran domin kawo ƙarshen rikicin na tafiya yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Trump zai janye yaki da Iran ba tare da cika wani burinsa ba

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump a wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Neman Larabawa su biya Trump kudi

Reuters ta rahoto cewa Leavitt ta yi bayanain ne da aka tambaye ta a wani taron manema labarai ko ƙasashen Larabawa za su taimaka wajen biyan kuɗin yaƙin.

Ta ce ba za ta yi gaggawar magana a madadin shugaba Donald Trump ba, amma ta ce wannan wani abu ne da Trump ke tunani a kai.

Al-Jazeera ta rahoto ta ce:

“Na yi imanin cewa wannan wani abu ne da shugaban ƙasa zai yi matuƙar sha’awar kiran su su yi,”

Batun tattaunawa da kasar Iran

Ta ƙara da cewa, abin da Tehran ke faɗa a bainar jama’a ya bambanta da abin da take faɗa wa jami’an Amurka a ɓoye, inda ta ce Iran ta amince da wasu daga cikin shawarwarin Washington a asirce.

“Duk da maganganun da ake yi a fili da kuma rahotannin da ba su da inganci, tattaunawa na ci gaba kuma tana tafiya da kyau. Abin da ake faɗa a fili ya sha bamban da abin da ake sanar da mu a ɓoye,”

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Inji ta.

Karoline Leavitt a wajen taro a Amurka
Mai magana da yawun fadar White House, Karoline Leavitt. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin Trump ga Iran

A baya, Trump ya yi gargadin cewa za a lalata cibiyoyin makamashi da rijiyoyin mai na Iran idan ba ta buɗe mashigar Hormuz ba.

Hakan na zuwa ne bayan Tehran ta bayyana shirin zaman lafiya na Amurka a matsayin wanda ba zai yiwu ba tare da kai hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila.

Batun sauyin gwamnati a Iran

A wani bayani da ya yi,Trump ya ce tattaunawa da Tehran na tafiya da kyau, har ma ya nuna cewa an riga an samu “sauyin gwamnati” a kasar

Ya ce:

“Mun riga mun samu sauyin gwamnati, idan ka duba, domin tsohuwar gwamnatin ta lalace kuma ta rushe. Sabuwar ma kusan haka take. Yanzu muna mu’amala da wasu mutane daban gaba ɗaya,”

Trump zai tsayar da yakin Iran

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump ta nuna alamun kawo karshen yakin Iran ko ba a bude mashigar Hormuz ba.

Kara karanta wannan

Iran ta shaidawa Amurka tanadin da ta yi wa sojojin da za su kutso cikin kasarta

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka wuce wata daya da fara yakin, alhali gwamnatin Trump bata son ya wuce mako hudu zuwa shida.

Rahotanni sun bayyana cewa Donald Trump ne ya sanar da hadimansa bukatar tsayar da yakin a wata tattaunawa da suka yi a White House.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng