Akwai Matsala: Sanatan Amurka Ya Gano Ramin da Ake Shirin Jefa Amurkawa a Yakin Iran
- Sanatan Amurka, Adam Schiff ya soki yunkurin sake ware Dala miliyan 200 domin ci gaba da yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Schiff ya nuna adawa da yunkurin 'yan Republican na zabtare kudaden da aka ware domin kula da lafiyar Amurkawa
- Ya kara da cewa shirin gwamnatin Trump na neman karin kudin yaki yana nufin kowanne iyali a Amurka zai bayar da kusan $1,400
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Sanatan jihar California, Adam Schiff ya fito fili ya nuna adawarsa da yunkurin gwamnatin Amurka na sake ware Dala miliyan 200 saboda yakin da kasar take yi da Iran.
Adam Schiff, ya yi gargadi cewa karin Dala biliyan 200 da ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ke nema domin yakin Iran na iya janyo zabtare kudaden kula da lafiyar iyalan Amurkawa.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa sanatan ya nuna adawa da wannan mataki, yana mai cewa Amurkawa ba su goyon bayan wannan yaki da a yanzu ya shafe sama da kwanaki 30.
Sanata ya soki shirin zabtare kudin lafiya
Schiff, wanda dan jam’iyyar Democrat ne, ya bayyana hakan ne bayan wani rahoto ya nuna cewa ‘yan Republican na duba yiwuwar rage kudaden kiwon lafiyar jama’a domin samun kudin yakin da kuma ayyukan tsaron bakin haure.
A wani sako da ya fitar domin martani kan yunkurin 'yan jam'iyyar Republican, Sanata Schiff ya ce:
“Yakin da ba kwa so, amma za a biya shi da rage kudin lafiyarku.”
Ya kara da cewa shirin gwamnatin Shugaba Donald Trump na neman karin kudin yaki yana nufin kowanne iyali a Amurka zai bayar da kusan Dala 1,400 domin ci gaba da kai hare-hare a Iran.
Schiff ya aika tambayoyi ga gwamnatin Trump

Kara karanta wannan
Sanatan Amurka ya karaya kan yaki da Iran, ya fadi abin da ya sa kasarsa rashin nasara
Sanata Schiff ya ce wannan wata matsala ce daban da za a jefa Amurkawa a ciki ba ya ga karin kudin da jama’a ke biya na man fetur da sauran kayayyaki da suka kara tsada sakamakon yakin.
A rahoton NBC News, Sanatan ya aika tambayoyi ga gwamnatin Trump, inda ya ce:
“Saboda me? Sabon jagora za a samar? Karin tsattsauran ra’ayi? Karin ribar Rasha? Karin farashin mai? Ko karin hadari ga sojoji da iyalansu?”

Source: Getty Images
Yadda sanatan ke sukar gwamnatin Trump
Sanatan ya kasance daya daga cikin masu sukar gwamnatin Trump, kuma ya taba zama daya daga cikin masu jagorantar zaman shari’a a lokacin da aka gurfanar da Trump a majalisar wakilai a wa’adinsa na farko.
Wannan batu na nuna yadda ake ci gaba da muhawara a Amurka kan yadda za a dauki nauyin yakin Iran, inda wasu ke nuna damuwa cewa talakawa za su fi shan wahala ta fuskar lafiya da tattalin arziki.
Iran ta musanta fara tattaunawa da Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake fitowa ta karyata ikirarin cewa an fara tattaunar sulhu don tsagaita wuta tsakaninta da Amurka/Isra'ila.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Bagaei, ya bayyana cewa kasar ba ta shiga wata tattaunawa da Amurka ko Isra'ila ba tun bayan fara yakin.
Sai dai ya bayyana cewa abin da ya faru shi ne Amurka ta gabatar da bukatar tattaunawa tare da wasu shawarwari, wadanda suka iso hannun Iran ta hannun wasu kasashe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

