Kasashe 8 Sun Dauko Hanya Mai Muhimmanci, Sun Yi Zama kan Yakin Iran da Amurka

Kasashe 8 Sun Dauko Hanya Mai Muhimmanci, Sun Yi Zama kan Yakin Iran da Amurka

  • Jordan da Rasha da kasashen yankin Gulf shida sun yi wani zama mai muhimmanci ta yanar gizo kan yakin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar musulunci ta Iran
  • Wannan na zuwa ne yayin a aka kwashe fiye da kwanaki 30 ana musayar wuta tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da kasar Iran
  • Taron, wanda ya gudana ta yanar gizo, ya faru ne karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Bahrain, Abdullatif bin Rashid Al Zayani.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Kasashen yankin Gulf da kasar Jordan da Rasha sun yi wani zama ta yanar gizo kan yakin da ke tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wannan musayar wuta da ke kara zafafa tsakanin kaashen uku na ci gaba da yin illa ga tattalin arzikin duniya, tare da jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin kunci.

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Harin Iran.
Yadda Amurka ke harba makamai daga jiragen ruwa zuwa kasar Iran Hoto: U.S Navy
Source: Getty Images

Kasashe 8 sun yi zama kan yakin kasar Iran

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa duba da barin wutar da ke faruwa, Kasashen Gulf da Jordan da Raaha sun yi tattaunawa ta musamman kam barazanar tsaro a Gabas ta Tsakiya.

An gudanar da wannan muhimmin taro ta yanar gizo tsakanin ministocin harkokin waje na kasashen yankin Gulf da suka hada da Saudi Arabia, Qatar, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain da Oman, tare da Jordan da kuma Rasha.

Taron ya gudana ne karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Bahrain, Abdullatif bin Rashid Al Zayani, kamar yadda Jordan News ta ruwaito.

Taron ya samu halartar babban sakataren Kungiyar Hadin Kan Kasashen Gulf (GCC), Jasem Mohamed Albudaiwi, yayin da ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, shi ma ya halarta.

Abubuwan da taron ya maida hankali

A cewar wata sanarwa daga GCC, taron ya mayar da hankali ne kan tattauna batun hare-haren da ake zargin kasar Iran na kai wa kasashen Gulf da Jordan da kuma nazarin sababbin abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Tchiani ya tsoma baki a yakin Iran da Isra'ila, yana zargin an kulla wa Nijar makirci

Taron ya nuna yadda kasashen yankin ke kokarin hada kai da abokan hulda domin fuskantar matsalolin tsaro da ke kara kamari, musamman dangane da rikicin da ya shafi Iran.

Haka kuma, halartar Rasha a wurin taron na nuna yadda manyan kasashen duniya ke sa ido da kuma shiga cikin al’amuran yankin domin nemo mafita.

Duk da cewa babu wata sanarwa da ke nuna matsayar da kasashen suka cimmawa a taron, amma dai ana hasahen kasashen sun fara nazari kan matakan da ya kamata su dauka.

Spain ta hana jiragen Amurka shiga yankinta

A wani labarin, kun ji cewa kasar Spain ta hana jiragen yakin Amurka amfani da sararin samaniyarta yayin da ake ci gaba da musayar wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministar tsaron kasar, Margarita Robles, ta bayyana cewa gwamnatin Spain ba za ta amince da amfani da sararin samaniyarta ko sansanonin soji ba domin ayyukan da suka shafi yakin Iran.

Wannan mataki zai tilasta jiragen yakin kasar Amurka su sauya hanyarsu yayin tafiya, duk da cewa Spain ta sassauta wannan doka ga jiragen kai daukin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262