Ana Shirin Yin Sulhu, Spain Ta Jikawa Amurka Aiki a Yakinta da Kasar Musulunci ta Iran

Ana Shirin Yin Sulhu, Spain Ta Jikawa Amurka Aiki a Yakinta da Kasar Musulunci ta Iran

  • Kasar Spain ta hana jiragen yakin Amurka amfani da sararin samaniyarta yayin da ake ci gaba da musayar wuta a yankin Gabas ta Tsakiyha
  • Wannan matakin da Spain ta dauka ya shafi yakin da hadin guiwar Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, wanda aka fara a karshen watan Fabrairun 2028
  • Hakan zai tilasta jiragen Amurka canza hanya domin kaucewa shiga yankin kasar Spain, lamarin da ake ganin ba zai yi wa kasar dadi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Spain - Yayin da aka shiga wata na biyu da fara yakin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kasar Spain ta kara daukar matakai don kaucewa shiga wannan rikici.

Kasar Spain ta sanar da hana jiragen sojin Amurka da ke da hannu a hare-haren da ake kai wa Iran amfani da sararin samaniyarta.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Amurka ta fadi lokacin ficewa daga Iran, ta jero nasarorin da ta samu

Pedro Sanchez.
Firaministan kasar Spain, Pedro Sanchez da wani jirgin yakin Amurka Hoto: Thomas Coex
Source: Getty Images

Kasar Spain ta jikawa Amurka aiki

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa wannan matakin ya kara tsaurara takunkumin da Spain ta riga ta dauka kan amfani da sansanonin sojinta na hadin gwiwa.

Ministar tsaron kasar, Margarita Robles, ta bayyana cewa gwamnatin Spain ba za ta amince da amfani da sararin samaniyarta ko sansanonin soji ba domin ayyukan da suka shafi yakin Iran.

Ta ce:

“Ba mu ba da izinin amfani da sansanonin soji ko sararin samaniya ga duk wani aiki da ya shafi yakin kasar Iran ba.”

Wannan mataki zai tilasta jiragen yakin kasar Amurka su sauya hanyarsu yayin tafiya, duk da cewa Spain ta ware jiragen kai daukin gaggawa daga wannan matakin.

Me yasa Spain ta dauki matakin?

Ministan tattalin arziki na Spain, Carlos Cuerpo, ya bayyana cewa matakin ya nuna kin amincewar kasar da yakin da aka kaddamar ba tare da sahalewar kasashe ba, kuma wanda ya saba dokokin kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Iran ta kai hari mai muni Saudi, ta raunata sojojin Amurka da jirginsu

Firaministan Spain, Pedro Sanchez, ya dade yana sukar yakin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran.

A gefe guda kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakan kakaba takunkumin kasuwanci kan Spain sakamakon wannan matsaya, cewar Channels tv.

Shigaban Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Nathan Howard
Source: Getty Images

Wannan lamari na nuna yadda rikicin siyasa ke kara tsananta tsakanin kasashen duniya dangane da yakin Iran, inda wasu ke goyon baya, wasu kuma ke adawa da shi.

A ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 ne Amurka da Isra'ila suka kai hare-haren hadin gwiwa kan kasar Musulunci ta Iran, lamarin da ya lakume rayukan dubban mutane zuwa yanzu.

Pakistan na shirin sulhunta Amuka da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Pakistan ta sanar da cewa za ta karɓi bakuncin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen yakin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaiq Dar, ya ce ƙasarsa na alfahari da amincewar da Amurka da Iran suka nuna mata wajen ba ada hadin kai a tattaunawar.

Shugaban Amurka, Donald Trump , bai yi magana kai tsaye kan tattaunawar da za a yi a Pakistan ba, amma ya bayyana cewa ana tattaunawa da Iran kuma suna samun ci gaba sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262