Fafaroma Ya Gaji da Yakin Iran/Isra'ila, Ya Fadi yadda Ubangiji ke Fushi da Shugabanni
- Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Leo XIV ya yi sake yin magana game da yakin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
- Fafaroma ya ce Allah ba ya karɓar addu’o’in shugabannin da ke tayar da yaƙe-yaƙe, yana mai cewa hannayensu sun cika da jini
- Yayin bikin Palm Sunday, ya ce Yesu mai son zaman lafiya ne, kuma ba za a yi amfani da shi wajen halatta yaƙi ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rome, Italy - Fafaroma Pope Leo XIV ya bayyana damuwa game da ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Fafaroma ya bayyana cewa Allah ba ya sauraron addu’o’in shugabannin da ke tayar da yaƙe-yaƙe, yana mai cewa hannayensu sun cika da jini.

Source: Facebook
Abin da Fafaroma ya ce kan yakin Iran
Ya yi wannan furuci mai ƙarfi yayin da yaƙin Iran ya shiga wata na biyu a yankin Gabas da Tsakiya, cewar Reuters.
Da yake jawabi ga dubban mutane a lokacin bikin Palm Sunday, Fafaroman ya ce ba za a yi amfani da Yesu wajen halatta yaƙi ba.
Ya ce:
“Wannan shi ne Ubangijnmu: Yesu Sarkin Salama, wanda ke ƙin yaƙi, kuma babu wanda zai iya amfani da shi wajen halatta yaƙi.”
Ya ƙara da cewa Yesu ba ya sauraron addu’ar masu ta da yaƙe-yake da fitintinu a duniya.
Fafaroman ya kuma ambaci wani sashen Littafi Mai Tsarki inda aka ce, “Ko da kuka yi addu’o’i da yawa, ba zan saurara ba, domin hannayenku sun cika da jini.” Wannan ya ƙara bayyana matsayinsa kan rikicin.
Ko da yake bai ambaci sunan wani shugaba ba, ya ci gaba da ƙara sukar yaƙin Iran a ‘yan makonnin nan. Ya kuma yi kira da a tsagaita wuta nan take domin dakatar da rikicin.

Source: Facebook
Yakin Iran/Isra'ila: Shawarar da Fafaroma ya bayar
A baya-bayan nan, ya bayyana cewa hare-haren sama ba sa bambancewa tsakanin fararen hula da sojoji, don haka ya ce ya kamata a haramta irin waɗannan hare-hare gaba ɗaya.
Wasu jami’an Amurka sun yi amfani da kalaman addinin Kirista wajen kare hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila kan Iran da aka fara ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya ƙara tsananta rikicin, cewar rahoton Metro UK.
Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya jagoranci addu’a inda ya roƙi a yi amfani da ƙarfi mai tsanani kan waɗanda ya ce ba su cancanci jin ƙai ba.
Fafaroman ya kuma tuna wani labari daga Littafi Mai Tsarki inda Yesu ya hana mabiyinsa amfani da takobi lokacin da ake kama shi kafin a gicciye shi.
Fafaroma ya yi wa'azi kan yakin Iran da Isra'ila
An ji cewa bayan shafe wata daya ana luguden wuta a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila, Fafaroma Leo ya fito ya yi magana ga shugabanni.
A wani bayani da ya yi, Fafaroman ya bukaci kasashen da suke gwabza yakin su nemi mafita ta hanyar tattaunawa maimakon kai hare-hare.
Haka kuma, ya bayyana cewa ba zai iya shiru ba a daidai lokacin da bama-bamai ke kara sauka kan al'umma a kasashen da ke yaki da juna.
Asali: Legit.ng

