Iran Ta Fadi Shirin da Ta Yi na Tunkarar Sojojin Amurka, Ta Gano Makircin Trump
- Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi magana kan makircin kasar Amurka
- Ghalibaf ya ce sojojin kasar sun shirya karbar sojojin Amurka, yana zargin suna shirin kai hari a boye duk da ikirarin tattaunawa
- Ya soki Trump kan maganar sulhu da Iran, yana cewa Amurka na aika sakon zaman lafiya amma a gefe guda tana shirin kai farmaki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana damuwa game da munafurcin Amurka.
Ghalibaf ya bayyana cewa sojojin kasar sun shirya tsaf domin fuskantar duk wani zuwan sojojin Amurka a kasar a yakinta da Isra'ila.

Source: Getty Images
A cewar rahoton Al Jazeera, Ghalibaf ya soki tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, kan nuna aniyar tattaunawa da Iran amma a boye yana shirin kai hari.
Amurka ta shirya tura sojoji Gabas ta Tsakiya
Wannan martani na Iran na zuwa ne bayan shirin da Amurka ta yi na kara tura sojoji zuwa yankin Gabas ta Tsakiya a yakin da ake yi.
Rundunar sojojin Amurka na duba yiwuwar tura karin sojoji 10,000 zuwa Gabas ta Tsakiya sakamakon rikicin da ake yi a yankin.
Gwamnatin Donald Trump na son karin karfin sojan Amurka yayin da ake kokarin tilasta yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Iran.
Fadar White House ta gargadi Iran cewa Amurka na shirin daukar mataki mai tsauri idan ba a amince da yarjejeniyar gama yaki ba.

Source: Getty Images
Abin da Iran ke zargin Amurka na yi
Ghalibaf ya ce sun gano yadda Amurka ke ci gaba da yaudarar cewa ana tattaunawa a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin shirya kai farmaki ta ƙarƙashin ƙasa.
Ya ce:
“Abokin gaba na aikewa da sakon tattaunawa a fili, amma a boye yana shirin kai farmaki ta kasa.”
"Ya kara da cewa sojojin Iran na jiran zuwan Amurkawa, mutanenmu na jiran zuwan sojojin Amurka a kasa domin su kona su."

Kara karanta wannan
Tchiani ya tsoma baki a yakin Iran da Isra'ila, yana zargin an kulla wa Nijar makirci
Tun da farko a yau, kafafen yada labarai na Amurka sun ruwaito cewa Pentagon na shirye-shiryen kai hare-haren kasa a Iran na tsawon makonni masu yawa.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da rundunar sojin Amurka ta sanar da isowar karin sojoji 3,500 daga rundunar 31st Marine Expeditionary Unit zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan mataki ya kara jawo maganganu kan yakin da ake yi da ya ki ci ya ki cinyewa wanda ya shafe wata guda kenan ana yi, cewar BBC.
Iran ta ba Amurka, Isra'ila wa'adin awa 48
A wani labarin, an ji cewa dakarun 'Islamic Revolutionary Guard Corps' a Iran watau IRGC ta yi gagarumar barazana ga Amurka da Isra'ila a yakin da ake yi.
IRGC ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan hare-haren da suka lalata wasu jami’o’i a Iran.
Ta bukaci Amurka ta yi Allah-wadai da harin kafin wa’adin da aka sanya, tare da gargadin ma’aikata da dalibai su guji kusantar harabar jami’o’i.
Asali: Legit.ng
