Yaƙi Ya Kacame, Sojojin Amurka na Shirin Kutsa wa cikin Iran

Yaƙi Ya Kacame, Sojojin Amurka na Shirin Kutsa wa cikin Iran

  • Yakin da Amurka da Isra'ila suka jawo a Gabas ta Tsakiya bayan kashe jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei na shirin ƙara ƙazanta
  • Wani rahoto ya bankaɗo cewa Amurka na shirin turo sojoji domin kai hare-haren ƙasa a Iran na tsawon makonni
  • Ana sa ran hare-haren ba za su kai ga cikakken mamaya ba, sai dai farmaki na musamman a wasu muhimman wurare

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America– Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) na shirye-shiryen gudanar da wasu hare-haren ƙasa a ƙasar Iran da za su iya ɗaukar makonni.

Wasu jami’an Amurka da ba a bayyana sunayensu ba suka tabbatar da shirin da ake yi yayin da yakin ya ke ƙoƙarin sauya salo tun bayan da aka fara shi.

Kara karanta wannan

"Kada ku ba makiya dama": Iran ta sabunta gargadi ga ƙasashen Gabas ta Tsakiya

Amurka ta fara shirin kutsa wa cikin Iran
Shugaban kasar Amurka Donald Trump a yayin taro Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Reuters ta wallafa cewa wasu jami'an tsaron Amurka sun ce yiwuwar wannan farmaki ba zai kai ga cikakken mamaya ba, amma zai haɗa da kai hare-hare na na musamman.

Amurka za ta aika dakarun Iran

Al-Jazeera ta ruwaito majiyoyin sun bayyana cewa shirin Pentagon zai mayar da hankali ne kan kai hare-hare na gaggawa da ƙananan rundunoni za su jagoranta, maimakon shiga yaƙin gaba ɗaya.

Sai dai rahoton ya ce har yanzu ba a tabbatar ko Shugaban Amurka, Donald Trump, zai amince da dukkanin tsare-tsaren Pentagon ba, ko kuma wani ɓangare daga ciki, ko ma ya ƙi su gaba ɗaya.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da rundunar sojin Amurka ta sanar da isowar sojoji 3,500 daga rundunar 31st Marine Expeditionary Unit a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta zama barazana a kan Hormuz

A wani ɓangare kuma, Donald Trump ya buƙaci Iran ta amince da an ci ta da yaki, tare da yin barazanar sakin wuta a kanta idan har ta ci gaba da hana zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Yaki zai fadada: Kasar Afrika 1 tilo ta fito za ta taya Isra'ila yakar Iran

Amurka tana gargaɗin Iran ta amince an ci ta da yaki
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Getty Images

Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, kuma duk wani rikici a yankin na iya yin tasiri ga tattalin arzikin duniya baki ɗaya.

Tun bayan da Iran ta sanya takunkumin wucewa ta mashigar hankalin duniya ya tashi, inda Donald Trump ke neman a taya tilasta bude wajen.

An gano tallafin Rasha ga Iran

A baya, kun samu labarin cewa kasashen Turai sun bayyana zarge-zargensu kan Rasha game da tuhumarta da ake yi na taimaka wa Iran a yakin da ake yi.

Rahotanni sun nuna cewa Rasha na bai wa Iran bayanan leken asiri da fasahar yaki, ciki har da amfani da jiragen marasa matuki wajen ci gaba da kare kanta daga Yahudawa da Nasara.

Sai dai Marco Rubio ya rage muhimmancin hadin gwiwar, yana cewa ba ta kawo cikas ga ayyukan Amurka ba, yayin da ƙasarsa ke shirin kai sababbin hare-hare cikin ƙasar Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng