Magana Ta Kare: Amurka Ta Fadi Lokacin Ficewa daga Iran, Ta Jero Nasarorin da Ta Samu

Magana Ta Kare: Amurka Ta Fadi Lokacin Ficewa daga Iran, Ta Jero Nasarorin da Ta Samu

  • Kasar Amurka ta yi magana game da nasarorin da samu yayin yakin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
  • Amurka ta ce ta cimma yawancin burinta a yakin Iran, amma za ta ci gaba da kai hare-hare na ɗan lokaci
  • Mataimakin shugaban Amurka ya ce farashin mai ya tashi sakamakon rikicin, amma ya tabbatar da cewa hakan na wucin gadi ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya yi magana kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Israila.

JD Vance ya ce nan ba da jimawa ba Amurka za ta janye daga yakin da ake yi saboda nasarorin da ta cimma a kankanin lokaci.

Amurka ta yi karin haske kan karkare yaki da Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Vance ya bayyana haka ne yayin wata hira da mai gabatar da shirin Podcast mai ra’ayin mazan jiya, Benny Johnson wanda Al Jazeera ta bibiya.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fara kai Turkiyya wuya, ta gargadi kasar kan yakinta da Iran

Donald Trump ya magantu kan farashin fetur yanzu

Wannan ba shi karon farko ba da Amurka ke fatan kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Iran da Ista'ila a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Donald Trump, ya yi magana kan tasirin da yakin Iran da Isra'ila ke yi kan farashin mai a duniya.

Trump ya ce farashin mai zai ragu sosai bayan yaƙin Iran ya ƙare, duk da tsadar man fetur da ake fama da ita yanzu.

Yaƙin da ake yi da Iran ya haifar da tashin farashin mai, yayin da jiragen dakon mai suka makale a mashigan Hormuz.

Iran: Amurka ta fadi nasarar da ta cimma

Vance ya bayyana cewa Amurka ta riga ta cimma mafi yawan manufofinta na soja, amma Donald Trump yana shirin ci gaba da yakin na wani ɗan lokaci domin tabbatar da an raunana gwamnatin Iran sosai.

Ya ce:

“Shugaban kasa zai ci gaba da wannan aiki na ɗan lokaci domin tabbatar da cewa bayan mun fice, ba za mu sake dawowa irin wannan rikici ba na dogon lokaci.

Kara karanta wannan

Gargadi mai tsauri da Trump ya yi ga kasar Iran kan sharudansa na zaman lafiya

“Muna bukatar mu rage karfin gwamnatin Iran sosai na tsawon lokaci mai yawa, kuma wannan shi ne babban dalilin da ya sa ake ci gaba da wannan yaki.”

Ya amince cewa farashin man fetur ya karu sakamakon rikicin, amma ya bayyana cewa wannan na wucin gadi ne kuma zai ragu nan gaba kadan.

A cewarsa:

“Wannan kawai abu ne na wucin gadi ga wani rikici da ake sa ran zai kasance na ɗan lokaci kadan ne.”

Ya kuma jaddada cewa Amurka ba ta da niyyar zama a Iran na tsawon lokaci, yana mai cewa gwamnati za ta kammala aikin da take yi sannan ta fice cikin gaggawa.

Trump zai afkawa Cuba da yaki

Tun farko, mun ba ku labarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump na ci gaba da maganganu kan kawo karshen yakin da suke yi da Iran, sai dai ya ce za su kai hari a Cuba a nan gaba.

Shugaba Trump ya yaba wa sojojin Amurka kan yadda suka shiga har kasar Venezuela suka kama shugaban kasar da matarsa suka tafi da su.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban Amurkan ya yi magana ne yayin wani taro da aka gudanar a birnin Miami na kasar Amurka game da tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.