Lamari Ya Girma: An Maka Trump a Kotu bayan Bankada a Takardun Eipstein

Lamari Ya Girma: An Maka Trump a Kotu bayan Bankada a Takardun Eipstein

  • Wasu daga cikin mutanen da sunayensu da hotunansu suka fito a takardun Jeffrey Epstein sun kai karar gwamnatin Amurka da Google
  • Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta fitar da miliyoyin takardu da suka hada da bayanan wadanda aka boye amma aka fallasa
  • Wadanda abin ya shafa sun ce hakan ya jawo masu bacin suna a tsakanin mutane da kuma barazana daga jama’a da dama a fadin duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wadanda suka tsinci kansu a laifukan marigayi mai aikata lalata, Jeffrey Epstein sun shigar da kara a kotu.

Mutanen sun yi korafi ne a ranar Alhamis 26 ga watan Maris 2026 kan Gwamnatin Amurka da kamfanin Google.

An maka gwamnatin Trump a kotu kan Epstein
Marigayin dan kasuwa, Jeffrey Epstein da Donald Trump a tsibirin Palm da ke Florida. Hoto: Davidoff Studios.
Source: Getty Images

Rahoton The Hindu ya bayyana cewa mutanen sun nuna damuwa kan fallasa sunayensu a cikin wadanda abin ya shafa a cikin takardu da aka wallafa a intanet.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka, Trump fa fadi kasar da zai tafi ya nemi shugaban kasa

Yadda ma'aikatar shari'a ta fitar da takardu

Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta fitar da sama da takardu miliyan uku a watan Janairun 2026 da suka shafi binciken Jeffrey Epstein, ciki har da alakar sa da manyan mutane.

Sai dai jami’an gwamnati sun shiga cikin rudani bayan da aka gano cewa sunayen wadanda abin ya shafa wadanda ya kamata a boye sun bayyana ba tare da an rufe su ba.

Masu karar sun ce ma’aikatar shari’a ta fallasa kusan mutane 100 da suka tsira daga wannan mai laifin, inda aka wallafa bayanansu na sirri tare da bayyana su ga duniya.

Sun kara da cewa ko da bayan gwamnati ta amince cewa hakan ya saba wa hakkokin su tare da janye bayanan, kamfanonin intanet kamar Google suna ci gaba da sake wallafa su.

A cewar karar, Google na nuna bayanan sirri na wadanda abin ya shafa a sakamakon bincike da kuma cikin bayanan da na’urar AI ke samarwa.

Kara karanta wannan

Matakai 4 da Najeriya ta dauka bayan fara yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Kazalika, an gano hotuna tsirara da dama a cikin takardun da ke dauke da fuskokin mutane, cewar Leadrship.

Takardun Epstein na ci gaba da tayar da kura
Marigayi attajirin dan kasuwa a Amurka, Jeffrey Epstein. Hoto: T@nicksortor.
Source: Twitter

Yaushe Epstein ya mutu a gidan yari?

An yanke wa Epstein hukunci a shekarar 2008 kan neman lalata da ‘yan mata masu kananan shekaru, amma ya mutu a gidan yari a New York a shekarar 2019 kafin a gurfanar da shi kan zargin safarar mata, cewar Vanguard.

Masu karar sun ce wadanda suka tsira yanzu suna fuskantar matsala, inda mutane ke kiransu, tura musu sakonni, yi musu barazana da kuma zarginsu da hadin baki da Epstein.

Sun kuma yi zargin cewa gwamnati ta karya dokar sirri ta 1974, yayin da Google ya karya dokokin California kan kutsawa cikin sirri, jawo damuwa ta tunani da kuma gudanar da harkoki ba bisa ka’ida ba.

An gano alakar Epstein da Boko Haram

A baya, kun ji cewa wani sabon bincike ya danganta marigayi Jeffrey Epstein da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak da Boko Haram.

Rahoton ya ce an yi amfani da tattaunawar tashoshin jiragen ruwa a Lagos da Badagry, da kuma fasahar tsaro, domin samun moriyar kasuwanci.

Binciken ya yi zargin cewa hanyoyin tsaro da jarin da aka zuba sun bai wa bangarorin damar cin gajiyar rashin zaman lafiyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.