Iran Ta Gano Masu ba Sojojin Amurka Mafaka, Ta Sha Alwashin Ruguza Su da Hare Hare

Iran Ta Gano Masu ba Sojojin Amurka Mafaka, Ta Sha Alwashin Ruguza Su da Hare Hare

  • Kasar Iran ta yi gargadi mai tsauri ga wasu mamallakan otal otal a yankin da take gwabza yaki da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Ta ce duk otal-otal da ke daukar sojojin Amurka a yankin za su zama halastattun wuraren kai hare-hare yayin rikicin da ke gudana
  • Kakakin rundunar Iran ya ce idan sojojin kasar Amurka suka fake a otal, hakan na nufin wurin ya zama makasudin kai hari kai tsaye

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta yi gargadi ga sojojin Amurka da wasu otal otal a yakin da ake yi tsakaninta da Isra'ila wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Kasar Iran ta bayyana cewa za ta rika kai hare-hare kan dukkan otal-otal da ke daukar sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya yayin rikicin da ke gudana.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban kamu, an gano mutane da ke yada sirrinta ga makiya a yaki da Isra'ila

Iran ta sake gargadin masu ba sojojin Amurka mafaka a yaki
Shugaban Amurka, Donald Trump da jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Reza B, Andrew Caballero-Reynolds.
Source: Twitter

Gargadin Iran ga masu tallafawa sojojin Amurka

Kakakin rundunar sojin Iran, Abolfazl Shekarchi, ya ce idan sojojin Amurka suka shiga otal, to wurin ya zama na Amurka kuma zai fuskanci hari mai tsanani, cewar Al Jazeera.

Ya kara da cewa ba zai yiwu Iran ta zuba ido tana kallon Amurka na kai mata hari ba tare da mayar da martani ba a wuraren da suke ba inda ta ce duk otal da ke ajiye sojan Amurka zai fuskanci hari kai tsaye.

Rikicin ya fara ne a ranar 28 ga Fabrairun 2026 bayan harin hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila ya kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Har ila yau, harin ya yi sanadiyyar kashe wasu manyan jami'an tsaron Iran wanda daga bisani ta mayar da martani kan Isra'ila da wasu ofishin jakadancin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Tun daga lokacin, Iran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan Isra’ila da muradun Amurka a yankin.

Kara karanta wannan

Iran ta tanadi dakaru miliyan 1 a shirin yin gaba da gaba da sojojin Amurka

Iran ta fusata kan yadda otal ke ajiye sojojin Amurka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei yayin tattaunawa a Tehran. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Iran ta gano mafakar sojojin Amurka

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya zargi sojojin Amurka da fakewa a otal-otal da ofisoshi a kasashen Gulf.

Ya ce tun farkon yakin, sojojin Amurka sun bar sansanoninsu na soja domin boyewa a wuraren jama’a, abin da ya kira amfani da mutane a matsayin garkuwa.

Rahotanni sun ce Iran ta aika da gargadi mai tsauri ga otal-otal musamman a Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain kan karbar bakuncin sojojin Amurka.

Haka kuma, an bayyana cewa Iran ta gano irin wadannan wurare da ake zargin sojojin Amurka na amfani da su a kasashen Syria, Lebanon da Djibouti.

Sai dai kasashen yankin Gulf sun sha musanta zargin Iran cewa suna bai wa Amurka damar kai hare-hare daga kasashensu, cewar rahoton Punch.

Gargadin Amurka ga Iran kan sharudan zaman lafiya

A baya, mun ba ku labarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargadi mai tsauri ga hukumomi a Iran kan bijirewa sharudan zaman lafiya..

Kara karanta wannan

Duk da gargadin Iran ga Trump, Amurka ta yi biris kan matakin da ta shirya dauka

Trump ya yi barazanar cewa idan Iran ta ki amincewa da wadannan sharuda, matakin Amurka zai tsananta kuma 'ba zai yi kyau ba'.

Shugaba Trump ya kuma soki NATO yana cewa kasashen kungiyar ba su taimaka ba a yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.