Duk da Gargadin Iran ga Trump, Amurka Ta Yi Biris kan Matakin da Ta Shirya Dauka
- Rundunar sojojin Amurka na duba yiwuwar tura karin sojoji 10,000 zuwa Gabas ta Tsakiya sakamakon rikicin da ake yi a yankin
- Gwamnatin Donald Trump na son karin karfin sojan Amurka yayin da ake kokarin tilasta yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Iran
- Fadar White House ta gargadi Iran cewa Amurka na shirin daukar mataki mai tsauri idan ba a amince da yarjejeniyar gama yaki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Wani rahoto ya nuna cewa Amurka na nazarin yiwuwar tura karin sojoji 10,000 zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan mataki ya biyo bayana ci gaba da yaki da ake yi tsakanin Iran da kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Source: Facebook
Rahoton New York Post ya ce wannan karin sojojin zai hada da dakaru na kasa da kuma manyan motocin yaki, kuma zai kara ne kan dubban sojojin da aka riga aka tura yankin.

Kara karanta wannan
Trump ya faɗi abin da Iran ta bukata a gare shi a yaki, ya kara mata wa'adin kwanaki 10
Gargadin da Iran ta yi ga Amurka
Tun farko, kasar Iran ta yi martani mai zafi game da shirin Amurka na kara tura dakarun sojoji zuwa yakin Gabas ta Tsakiya da ake gwabza yaki a yankin.
Iran ta gargadi Amurka kan shirinta tana cewa tana sa ido sosai kan dukkan motsin rundunar Washington duba da shirin da kasar ke yi
Kakakin majalisa a Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa duk wani kuskure daga Amurka na iya haifar da mummunan sakamako a yankin.
Dalilin Amurka na tura sojoji Gabas ta Tsakiya
A cewar majiyoyi, wannan mataki zai ba Donald Trump karin zabin amfani da karfin soja, ciki har da yiwuwar tura sojoji kai tsaye a kasa domin matsa wa Iran ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya.
Sai dai ba a bayyana takamaiman wurin da za a tura karin sojojin ba, amma ana hasashen za su kasance kusa da Iran da muhimman wuraren ruwa kamar mashigar Hormuz.
Fadar White House ta ce duk wani bayani kan tura sojoji zai fito ne daga hukumomin tsaro, yayin da Pentagon ya ki yin karin bayani kan lamarin.
Amurka ta yi ikirarin cewa karin dakarun a Gabas ta Tsakiya zai taimaka wa sojojintada kuma kara masu kaimi wurin tabbatar da cewa sun samu nasara a yakin da ake yi a yankin.

Source: Getty Images
Gargadin Fadar White House ga kasar Iran
A gefe guda, mai magana da yawun fadar White House, Karoline Leavitt, ta gargadi Iran cewa Shugaban Amurka ba ya wasa, yana kuma shirye ya dauki mataki mai tsauri idan Iran ta ki amincewa da yarjejeniya.
Ta ce duk wani karin tashin hankali daga Iran zai kara haddasa martani mai tsanani daga Amurka, tana mai cewa kasar Iran ta riga ta fuskanci mummunar asara a bangaren soji, cewar Turkiye Today.
Rahotanni sun kuma nuna cewa Amurka na nazarin yiwuwar amfani da sojoji domin kare muhimman wurare kamar mashigar Hormuz da kuma wasu muhimman kadarori na Iran.
Trump ya magantu kan karkare yakin Iran
A baya, an ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tasirin da yakin Iran da Isra'ila ke yi kan farashin mai a duniya.
Trump ya ce farashin mai zai ragu sosai bayan yaƙin Iran ya ƙare, duk da tsadar man fetur da ake fama da ita yanzu.
Yaƙin da ake yi da Iran ya haifar da tashin farashin mai, yayin da jiragen dakon mai suka makale a mashigan Hormuz.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

