Ba Wasa: Iran Ta Kaddamar da Hare Hare Masu Zafi kan Amurka da Isra'ila
- Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da hare-hare kan muhimman wurare na Amurka da Isra'ila
- IRGC ta farmaki wasu sansanonin sojoji na Amurka yayin da ta kaddamar da rukuni na 83 na hare-haren ramuwar gayyan da take kai wa
- Rundunar ta bayyana cewa ba za ta sassauta ba har sai ta sanya sun girbi sakamakon munanan ayyukan da suka yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da gudanar da farmaki karo na 83 na "Operation True Promise 4"
Rundunar IRGC ta farmaki muhimman cibiyoyin soja na Amurka da Isra'ila a faɗin yankin da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.

Source: Twitter
Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen hulɗa da jama'a na IRGC, ya fitar a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026.
IRGC ta sadaukar da farmakin da ta kai
A cewar IRGC, an sadaukar da wannan farmakin ne ga "mutanen kirki na yankin Kudancin ƙasar da ke Arewacin Tekun Fasha (Persian Gulf)" kuma an gudanar da shi ne ƙarƙashin kalmar sirri mai albarka ta "Ya Aba Abdullah Al-Hussein (AS)."
Hare-haren sun nufi rukunin muhimman kadarori na dakarun Amurka da na gwamnatin Isra'ila.
Wadanne wurare aka farmaka?
Daga cikin wuraren da aka farmaka akwai rumbunan adana mai a Ashdod, wurin zama na ma'aikatan soja a Modi'in, da kuma cibiyar musayar bayanan sirri ta sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Haka zalika, IRGC ta farmaki sansanonin sojojin Amurka na Al-Dhafra da Al-Udeiri, tare da rumbunan gyara da adana jiragen sufuri da jirage marasa matuka a sansanin sama na Ali Al-Salem.
Sauran wuraren da aka farmaka sun haɗa da rumbunan man jiragen yaƙi na dakarun Amurka, da kuma wurin gyara na'urar kariya ta makamai masu linzami na Patriot a sansanin Sheikh Isa, shafin cameroonintelligencereport ya kawo labarin.
Makaman da kasar Iran ta harba
Sanarwar ta IRGC ta nuna cewa an yi amfani da makamai na zamani a farmakin, waɗanda suka haɗa da makamai maau linzami masu cin dogo da matsakaicin zango.
Ta ƙara jaddada cewa an kai waɗannan hare-haren martani cikin "cikakkiyar nasara da yardar Allah."
A cikin sanarwar, IRGC ta bayyana tasirin hare-haren da ake ci gaba da kaiwa kan rayuwar yau da kullum ta mazauna Isra'ila, inda ta ce "zama cikin kuwwar ƙararrawar gargaɗi da daɗewa a cikin dakunan fakewa ya zama al'ada ta yau da kullum ga Yahudawa."

Source: Twitter
IRGC ta kammala da wani gargaɗi mai tsauri:
"Kamar yadda muka faɗa, za mu nemo ku, kuma da yardar Allah, za mu sa ku girbi sakamakon munanan ayyukan da kuka aikata."
Isra'ila ta kashe babban kwamanda a Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar tsaron Isra'ila (IDF), ta sanar da cewa ta hallaka wani babban kwamanda a Iran.

Kara karanta wannan
Ba sassauci: Iran ta ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila, ta farmaki muhimman wurare
Rundunar IDF ta ce ta kashe babban kwamandan sojojin ruwa na rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), Alireza Tangsiri.
An kashe Alireza Tansgiri ne a wani harin Amurka da Isra'ila a yankin gabar teku na Bandar Abbas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

