Yan Isra’ila Sun Fara Gajiya da Halin Netanyahu, Sun Soke Shi kan Yaki da Iran
- Babban jagoran yan adawa a Isra'ila, Yair Lapid ya yi maganganu masu zafi game da yakin da kasar ke yi da Iran a Gabas ta Tsakiya
- Lapid ya zargi Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da jefa Isra’ila cikin matsalar tsaro mai tsanani a yakin da ake yi
- Ya ce sojojin Isra’ila sun yi yawa a fannoni da dama kuma ba su da isassun kayan aiki da sojoji wanda za su ba da gudunmawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Jagoran ‘yan adawar Isra’ila, Yair Lapid, ya caccaki Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan yaki da Iran
Lapid ya zargi Benjamin Netanyahu da jefa kasar cikin abin da ya kira babbar matsalar tsaro yayin da yaki ke kara kamari.

Source: Getty Images
An taso Netanyahu a gaban kan yakin Iran
Lapid ya bayyana hakan ne a rana ta 27 na yakin Isra’ila da Iran da Lebanon, inda ya ce sojojin kasar sun yi yawa a fannoni daban-daban, cewar Al Jazeera.
Jagoran yan adawa ya tabbatar da cewa sojojin kasar kuma ba su da karfin ci gaba da yaki a lokaci guda musamman a irin wannan yanayi.
Ya ce:
“Matukan jiragenmu da mayaƙanmu suna rubuta tarihi mai girma ga Isra’ila… amma ana tura rundunar soji har ta kai iyakarta, har ma ta wuce.”
Ya kara da cewa gwamnati ta bar sojojin cikin wani hali na rauni da rashin kulawa a fagen daga.

Source: Facebook
Zargin da Lapid ke yi wa Netanyahu
Lapid ya ce gwamnati na tura sojoji su yi yaki a fannoni da dama ba tare da tsari mai kyau ba, babu wadatattun kayan aiki, kuma ba su da isassun sojoji.
Ya nuna cewa rundunar sojin Isra’ila na fuskantar matsin lamba mai tsanani yayin da take yaki a wurare da dama ciki har da Gaza, Lebanon da Syria, tare da rikicin da ya shafi Iran.
Ci gaba da gudanar da wadannan hare-hare ya sa ana yawan dogaro da sojojin ajiya, yayin da ake fama da gibin daukar sababbin sojoji.
Wannan gargadi na zuwa ne a lokacin da martanin Iran da karuwar rikice-rikice a yankin ke kara tsananta yakin.
Rashin isassun sojoji da kayan aiki yayin da ake ci gaba da yaki na iya haifar da matsaloli a tsarin rundunar sojin na dogon lokaci, cewar Times of Israel.
Bayanin Lapid ya nuna cewa tsawaita yaki a fannoni da dama tare da shigar Iran na iya kai karfin sojin Isra’ila ga iyaka.
Isra'ila ta shiga jimami bayan rashin nasara
A wani labarin, an ji mayakan Hezbollah da dakarun sojojin Isra'ila na ci gaba da yin ba ta kashi a wasu yankuna da ke Kudancin Lebanon.
A wani artabu da aka yi tsakanin bangarorin biyu, mayakan Hezbollah sun samu nasarar hallaka wani sojan Isra'ila har lahira.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi jimamin rashin sojan tare da aika sakon ta'aziyya ga iyalansa da yi masa addu'ar fatan alheri a kiyama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

