Yakin Iran/Isra’ila Ya Fara Sauya Salo, Jami’ai saga Rasha Sun Dura a Amurka

Yakin Iran/Isra’ila Ya Fara Sauya Salo, Jami’ai saga Rasha Sun Dura a Amurka

  • Jami’an kasar Rasha sun isa Amurka domin tattaunawa yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin kasashen Iran da kuma Isra'ila
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko tun bayan takaddamar yakin Ukraine da take yi da Rasha
  • Kasar Rasha ta sha musanta zargin taimaka wa Iran, tana mai cewa rahotannin kafofin watsa labarai ƙarya ne da aka kirkire su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wasu jami’an gwamnati daga Rasha sun isa Amurka domin gudanar da ganawa da takwarorinsu na Amurka.

Wannan ziyara ta fara ne a ranar Alhamis 26 ga watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki yayin da ake yaki tsakanin Iran da Isra'ila.

Rasha da Amurka za su yi zama ana tsaka da yaki
Shugaba Vladimir Putin ya samu tarba daga Donald Trump na Amurka a birnin Alaska. Hoto: Andrew Harnik.
Source: Getty Images

Musabbabin ganawar jami'an Rasha da Amurka

Ziyarar ita ce irinta ta farko tun bayan da dangantaka ta yi tsami sakamakon yakin Ukraine, wanda ya shafe shekaru ana yi tsakanin bangarorin biyu, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka

Mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov, ya bayyana cewa Rasha na fatan wannan mataki zai taimaka wajen farfado da hulɗar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa Shugaban ƙasar, Vladimir Putin, ya bayar da umarnin yadda za a gudanar da wannan tafiya, kuma za a ba shi cikakken bayani kan abin da aka tattauna.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da tattaunawar da Amurka ke jagoranta domin kawo karshen yakin Ukraine ta tsaya cak, ba tare da cimma matsaya ba.

Tun bayan dawowar shugaban Amurka, Donald Trump, Fadar White House, an gudanar da jerin tattaunawa amma ba a samu warware matsalar ba.

Rasha, wacce kawar kusa ce ga Iran, ana zarginta da goyon bayan gwamnatin Tehran a yakin da take yi da Amurka da Isra'ila, cewar rahoton Pearls and Irritations.

Rahotanni sun ce Rasha na shirin aika wa Iran jiragen yaki marasa matuka, amma Dmitry Peskov ya musanta wannan zargi.

Ya ce akwai ƙarya da dama da kafafen yada labarai ke yadawa, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da irin wadannan rahotanni.

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Jami'an Rasha sun isa Amurka domin tattaunawa
Shugaban Rasha, Vladimir Putin. Hoto: Vyacheslav PROKOFYEV.
Source: Getty Images

Yadda Rasha ke ci gaba da farmakar Ukraine

A wannan makon, Rasha ta kai daya daga cikin manyan hare-haren sama kan Ukraine, inda ta harba jirage marasa matuka 948 cikin awanni 24.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bukaci kawayen kasarsa su samar da karin makamai na kare sararin samaniya.

Ya gargadi cewa kasar na iya fuskantar karancin makamai, musamman yayin da Amurka ke mayar da hankali kan yakin da take yi da Iran.

A gefe guda, tattaunawar da aka fara a jihar Florida ta Amurka ba ta haifar da tabbacin tsaro da Ukraine ke nema ba har yanzu.

Ukraine na zargin Rasha kan yakin Iran

An ji cewa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya yi magana kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Zelenskiy ya ce kasarsa ta samu hujja karara cewa Rasha na bai wa Iran bayanan sirri, lamarin da zai kara tsawaita rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya ce Rasha na amfani da fasahar tattara bayanan sigina da hadin gwiwa da wasu kasashen yankin domin taimaka wa Iran wajen kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.