Isra’ila Ta Fara Kai Turkiyya Wuya, Ta Gargadi Kasar kan Yakinta da Iran
- Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadi ga Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki tsakaninta da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
- Erdogan ya bayyana damuwa ganin yadda yakin Iran da Isra'ila ya jefa Gabas ta Tsakiya cikin mummunan rikici
- Ya zargi Benjamin Netanyahu da fadada rikici zuwa kasashe kamar Lebanon da sauransu wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ankara, Turkey - Shugaban kasar Türkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya ja kunnen Isra'ila kan ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Erdogan ya gargadi cewa yakin da aka fara kan Iran na kara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici mai tsanani.

Source: Twitter
Erdogan ya caccaki Netanyahu kan yakin Iran
Erdogan ya yi wannan bayani ne yayin wani taron jam’iyyarsa a Ankara inda ya ce yakin ya jefa yankin cikin mawuyacin hali mafi muni cikin shekaru 100, cewar TRT World.
Ya ce:
“Yakin da aka fara da Iran na kara nutsar da yankinmu cikin jini da tashin hankali, inda yara da ba su da laifi ke fuskantar hare-haren makamai.”
Shugaban ya kuma zargi Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da fadada rikicin fiye da Iran zuwa wasu kasashe.
Ya bayyana cewa gwamnatin Netanyahu na kokarin aiwatar da shirin mamaye Lebanon a hankali, duk da karya dokokin kasa da kasa.
Erdogan ya jaddada cewa Türkiya ba za ta yi shiru ba kan wahalar da al’ummar yankin ke sha, yana mai cewa ba sa bambancewa tsakanin makwabta.
Ya ce:
“Ba za mu taba watsi da abokanmu da ‘yan uwarmu a lokacin wahala ba, kuma ba za mu yi shiru ba kan radadin da suke ciki.”

Source: Getty Images
Erdogan ya bayyana illar yakin Iran da Isra'ila
Shugaban ya kuma nuna damuwa kan yadda rikicin ke haddasa asarar rayuka, yana tambaya ko akwai bambanci tsakanin hawaye da ake zubarwa a biranen Iran da na sauran yankuna.
Ya kara da cewa duk da cewa rikicin na Isra’ila ne, amma sakamakonsa na shafar Musulmi da kuma bil’adama gaba daya, cewar Daily Sabah.
Erdogan ya kuma gargadi kan dabarun raba kawuna, yana mai cewa dole ne al’ummomin yankin su zauna tare bayan rikicin ya lafa.
Ya kuma soki hana gudanar da ibadar Sallah a Masallacin Kudus, yana mai cewa hakan cin zarafi ne ga Musulmi biliyan biyu.
A karshe, ya jaddada cewa Türkiya za ta ci gaba da bin manufofin diflomasiyya na zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba ga kowa.
Erdogan ya tattauna da shugaban Iran
A baya, kun ji cewa shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi waya da Shugaban Masoud Pezeshkian na Iran domin tattauna rikicin yankin.
Tayyib Recep Erdoğan ya jaddada cewa Türkiye na son buɗe ƙofa ga diflomasiyya domin rage tashin hankali a Gabas ta tsakiya.
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce makaman roka da suka shiga sararin samaniyar Türkiye ba daga Iran suka fito ba.
Asali: Legit.ng

