Gargadi Mai Tsauri da Trump Ya Yi ga Kasar Iran kan Sharudansa na Zaman Lafiya

Gargadi Mai Tsauri da Trump Ya Yi ga Kasar Iran kan Sharudansa na Zaman Lafiya

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargadi mai tsauri ga hukumomi a Iran kan bijirewa sharudan zaman lafiya
  • Ya yi barazanar cewa idan Iran ta ki amincewa da wadannan sharuda, matakin Amurka zai tsananta kuma 'ba zai yi kyau ba'
  • Trump ya kuma soki NATO yana cewa kasashen kungiyar ba su taimaka ba a yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan sharudan da ya gindaya game da zaman lafiya da Iran.

Trump ya gargadi masu tattaunawa a Iran da su dauki batun yarjejeniya da muhimmanci cikin gaggawa domin kawo karshen rikicin.

Trump ya sake gargadin Iran kan sulhu
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Trump ya tura gargadi ga Iran kan sulhu

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya bayyana masu tattaunawar Iran a matsayin “masu ban mamaki”, yana mai cewa suna rokon a kulla yarjejeniya amma a fili suna nuna akasin hakan.

Kara karanta wannan

Lissafi na neman kwacewa: Trump na son gama yaki da Iran cikin gaggawa

Ya ce:

"Masu tattaunawar Iran suna yin wasu abubuwa da bai kamata ba, hakan abin makai ne sosai, Suna “roƙon” mu mu kulla yarjejeniya, abin da ya kamata su yi tun da an murƙushe su a fagen yaƙi kuma babu nasara a tare da su, su yi abin da ya kamata.
“Ya kamata su dauki wannan lamari da muhimmanci cikin gaggawa kafin lokaci ya kure, domin idan hakan ta faru, babu dawowa baya, kuma ba zai yi kyau ba.”

Wannan gargadi ya biyo bayan sanarwar mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, wacce ta ce Trump na shirin daukar mataki mai tsauri idan Iran ta ki amincewa da yarjejeniyar.

Ta ce Iran ta riga ta sha kashi a fagen yaki, tana mai gargadin cewa duk wani ci gaba da rikici zai jawo karin martani mai tsanani daga Amurka.

Trump ya caccaki kasashen NATO
Shugaba Donald Trump na Amurka da Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu & Win McNamee.
Source: Getty Images

Yakin Iran/Isra'ila: Trump ya dura kan kasashen NATO

Trump ya kuma caccaki NATO, yana zarginsu da rashin taimakawa Amurka wajen tunkarar Iran a rikicinda ake yi.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Trump ya fadi masu kawo masa cikas a nasarar yaki da Iran

Ya kara da cewa Amurka ba ta bukatar taimakon NATO, amma ya bukaci a tuna da yadda kungiyar ta gaza taimakawa a wannan lokaci mai muhimmanci.

Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ke matsa lamba kan Iran ta bude mashigar Hormuz, tare da ikirarin cewa hare-haren soji sun raunana karfin Iran sosai.

A wani taro, Trump ya bayyana hare-haren da Amurka ke kai wa Iran a matsayin “aikin soja” maimakon “yaki”, yana mai cewa amfani da kalmar yaki na bukatar amincewar majalisa.

Majalisar Dinkin Duniya za ta binciki Amurka, Isra'ila

A wani labarin, an fahimci kwamitin Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da muhawara ta gaggawa kan harin makaranta a Iran da ya kashe yara 168.

Kasashen Iran, China da Cuba ne suka nemi zaman, suna zargin harin ya saba dokokin kasa da kasa da kuma jin ƙai na duniya wanda ya jawo ce-ceku-ce a tsakanin kasashe.

Rahoto ya nuna kuskuren harba makami na Amurka ne ya haddasa harin makarantar da ke Minab wanda ya jawo maganganu da Allah-wadai kan abin da ya faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.