An Bankado yadda Yakin Iran da Isra'ila Ya Ruguza Wani Babban Shiri na Amurka

An Bankado yadda Yakin Iran da Isra'ila Ya Ruguza Wani Babban Shiri na Amurka

  • Kudaden ruwa na karbar jinginar gida a Amurka sun tashi daga kashi biyar zuwa kashi shida sakamakon yakin da ake fafatawa da kasar Iran
  • Masanin tattalin arziki na Zillow ya yi gargadin cewa tashin farashin makamashi zai iya rage yawan sayar da gidaje a daukacin shekarar nan
  • Shugaba Donald Trump ya rage tsauraran dokoki domin saukaka wa yan kasa hanyoyin mallakar gidaje ta hanyar amfani da wasu fasahohi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Tasirin yaƙin da ake fafatawa da ƙasar Iran ya fara nuna kansa kai-tsaye a kasuwar gidaje ta ƙasar Amurka, inda aka samu gagarumin tashin kuɗaɗen ruwa na jinginar gida.

Kwana ɗaya kafin a fara kai hare-hare, matsakaicin kuɗin ruwa na jinginar gida na tsawon shekaru 30 yana matakin kashi 5.99, amma a yanzu ya haura zuwa kashi 6.5%.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka

Yakin Iran ya jefa Amurka cikin tsaka mai wuya ta fuskar mallakar gidaje.
Fuskar wani gida a San Fransisco, da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Smith Collection/Gado and Drew Angerer via Getty Images
Source: Getty Images

Kasuwar gidaje ta shiga garari a Amurka

Wannan tashin farashi ya kawo cikas ga tsammanin da ake da shi na sauƙaƙa wa mutane mallakar gidaje a wannan shekara, kamar yadda rahoton CNBC ya nuna.

Kafin ɓallewar yaƙin, an samu raguwar kuɗaɗen ruwa tare da ƙaruwar gidajen da ake sayarwa, abin da ya ba masu saye kwarin gwiwa da yakin mallakar gida a karamin lokaci.

Sai dai a makon jiya, aikace-aikacen neman jinginar gida sun ragu da kashi 5 sakamakon fargabar tsadar rayuwa da tashin farashin makamashi saboda yakin Gabas ta Tsakiya.

Babban masanin tattalin arziƙi na kamfanin Zillow, Mischa Fisher, ya bayyana cewa an tsara shekarar 2026 ne a matsayin 'shekarar sabunta fata' ga kasuwar gidaje, watau za a samu tallace-tallace da sayen gidaje da kusan kashi 4.3.

Masani ya hango matsala ga Amurka

To sai dai ya gargaɗi cewa:

“An samu rashin tabbas da ya kunno kai a kasuwar ta hanyar karuwar kudin makamashi da fargabar hauhawar farashi, wanda hakan ya jawo tsadar gidaje da rushewar lissafi.”

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Fisher ya yi gargaɗin cewa idan wannan yanayi ya ci gaba har zuwa watan Yuli, bukatar samun masu sayen gidaje za ta ragu zuwa kashi 2.33.

Mafi muni shi ne idan kuɗaɗen ruwa suka ci gaba da zama a matakin da suke yanzu tare da hauhawar rashin aikin yi, ana hasashen kasuwar gidaje za ta fuskanci raguwa da kashi 0.73 a ƙarshen shekarar 2026.

Shugaba Donald Trump ya rage dokokin jinginar gida don saukaka mallakar gida a Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi a fadar White House da ke Washington D.C. Hoto: Drew Angerer/Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya sauya dokokin jinginar gida

A gefe guda, Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan wani umarnin doka a makon jiya da nufin sauƙaƙa dokokin jinginar gida, musamman ga ƙananan bankuna, a cewar rahoton Yahoo Finance.

Wannan umarni yana ƙarfafa yin amfani da fasahar zamani kamar sa hannu ta intanet da kuma amfani da fasahar AI wajen kimanta darajar gidaje domin rage ɓata lokaci.

Gwamnatin Trump ta bayyana cewa sayen takardun jinginar gida na dala biliyan 200 da ta yi ya taimaka wajen rage wa masu sayen gidaje kuɗi kusan dala 5,000 ga kowane mutum.

Wannan yunƙuri dai na zuwa ne a matsayin tallafi ga ‘yan ƙasa a daidai lokacin da hauhawar farashi sakamakon yaƙin Iran ke neman daƙile muradin mutane na mallakar muhalli.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya janye kai mummunan hari Iran, ya fadi dalilan daukar matakin

Matsalar da Trump ke fuskanta a Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, sakamakon bincike ya nuna cewa kashi 27 kacal na Amurkawa ne suka goyi bayan harin da Donald Trump ya kai wa kasar Iran.

Ya zuwa yanzu an kashe sojojin Amurka da suka haura biyar yayin da wasu da dama suka jikkata, lamarin da ya sa farin jin Trump ya ragu da kashi 39 a kasarsa.

Amurkawa da dama sun bayyana aniyarsu ta janye wa daga goyon bayan Trump kan yaki da Iran idan har wasu abubuwa biyu suka faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com