Tofa: Ana cikin Yunkurin Tattaunawa, an Fallasa Mugun Nufin Netanyahu

Tofa: Ana cikin Yunkurin Tattaunawa, an Fallasa Mugun Nufin Netanyahu

  • Firaministan Spain, Pedro Sanchez, ya kausasa harshe kan takwaransa na kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan yakin da yake yi a Lebanon
  • Pedro Sanchez ya bayyana cewa Netanyahu na da wani mugun nufi da yake son cimmawa a yakin da yake yi
  • Hakazalika, Firaministan na Spain ya soki yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Madrid, Spain - Shugaban gwamnatin Spain, Pedro Sanchez, ya soki Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, kan yakin da yake yi a Lebanon.

Pedro Sanchez ya bayyana cewa Benjamin Netanyahu yana son yin barna mai girma a Lebanon.

Firaminitlstan Spain ya soki Benjamin Netanyahu
Firaministan Iran, Pedro Sanchez da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta ce Pedro Sanchez ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a gaban majalisa a ranar Laraba, 25 ga watan Maris 2026.

Wane mugun nufi Benjamin Netanyahu yake da shi?

Kara karanta wannan

Ana cikin yaki da Iran, an fallasa karyar da Netanyahu yake yi a Isra'ila

Shugaban na gwamnatin Spain ya bayyana cewa Netanyahu yana son ya yi barna mai girma a Lebanon kamar yadda ya yi a Gaza, tashar Reuters ta kawo rahoton.

Kalamansa na zuwa ne yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon yayin da suke shirin mamaye Kudancin kasar.

Shugaban Spain ya soki yakin Amurka, Isra'ila

Pedro Sanchez ya ce yaƙin da Amurka da Isra'ila suke yi da Iran “wani babban masifa ne,” wanda aka ƙaddamar domin “biya wa wasu sanannun mutane buƙatunsu.”

“Kuma duk wannan don me? Don a raunana dokokin ƙasa da ƙasa, a tada zaune tsaye a Gabas ta Tsakiya, a sake rura wutar rikici a Iraki da Lebanon, kuma a binne Gaza a ƙarƙashin baraguzan mantuwa da nuna ko-o-ho.”

- Pedro Sanchez

Pedro Sanchez ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa tana adawa da yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran, wanda ya nuna wani yanayi da ya “fi muni nesa ba kusa ba” fiye da mamayar Iraki ta shekarar 2003.

“Wannan ba yanayi ɗaya ba ne da haramtaccen yaƙin Iraki. Muna fuskantar wani abu da ya fi muni nesa ba kusa ba. Ya fi muni sosai. Tare da tasirin da zai iya zama mafi faɗi da zurfi."

Kara karanta wannan

An zo wajen: Trump ya yi magana kan tsagaita wuta a yakin Amurka, Isra'ila da Iran

- Pedro Sanchez

Pedro Sanchez ya ragargaji Netanyahu
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Spain ta soki Isra'ila kan yaki a Gaza

Shugaban gwamnatin ta Spain ya kasance ɗaya daga cikin shugabanni kalilan a Turai da suka yi tir da harin Amurka da Isra'ila a kan Iran, inda ya bayyana shi a matsayin wanda “ba shi da wani dalili na gaskiya.”

Spain ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Turai kalilan da suka ci gaba da yin Allah-wadai da ɗaukar mataki kan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Fiye da Falasɗinawa 72,000 ne aka kashe kuma yankuna masu faɗi a Gaza sun koma baraguzai a hare-haren Isra'ila tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta tun watan Oktoban 2025, Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 800 a kusan kowace rana ta hanyar karya yarjejeniyar da Trump ya shiga tsakani.

An yi ikirarin mutuwar Netanyahu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani dan jaridar Amurka, ya yi ikirarin cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bar duniya.

Kara karanta wannan

Dan jaridar Amurka ya yi ikirarin Netanyahu ya mutu har lahira

​Dan jarida daga kasar Amurka, Ethan Levins, ya yi ikirarin cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya rasu a ranar 8 ga Maris, 2026.

Levins ya kuma yi zargin cewa dan Firaministan, Yair Netanyahu, bai yi wani rubutu a dandalin X ba na tsawon kwanaki bakwai saboda zaman makoki ne Yahudawa ke yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng