Yakin Iran: An Yi wa Jirgin Isra'ila Ruwan Wuta bayan Tura Shi kai Hari

Yakin Iran: An Yi wa Jirgin Isra'ila Ruwan Wuta bayan Tura Shi kai Hari

  • Rahotanni sun nuna cewa kungiyar Hezbollah ta kai farmaki kan wani jirgin kasar Isra'ila yayin da ake tsaka da yakin Amurka a Iran
  • Kasashen Larabawa sun yi magana game da rawar da za su taka a yukurin sulhu da Iran da shugaba Donald Trump ya fara yi
  • Hukumomi sun tattabar da kai wani mummunan hari filin jirgin sama a kasar Kuwait, lamarin da ya kawo tsaiko a zirga-zirgar jama'a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Israel - Yakin Iran da Amurka/Isra'ila na cigaba da daukar zafi duk da maganar da shugaban kasa Donald Trump ya yi kan neman tsagaita wuta.

Da safiyar ranar Laraba, 25 ga Maris, 2026, kungiyar Hisbullah ta sanar da cewa ta kai farmaki kan jirgin yakin Isra'ila da ya nufi kai hari.

Kara karanta wannan

'Abin ya yi yawa,' Fafaroma ya yi wa Trump da Iran wa'azi mai ratsa zuciya

Jirgin yakin Isra'ila a sama
Wani jirgin yakin kasar Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa an kai wasu jerin hare-hare kasar Kuwait yayin da kasashen Larabawa suka yi magana kan sulhu da Iran.

Hezbollah ta farmaki jirgin Isra'ila

Jami'an yada labaran kungiyar Hezbollah sun sanar da cewa sun farmaki wani jirgin yaƙin Isra’ila a yammacin jiya yayin wani hari da ake zargin an yi niyyar kaiwa a Kudancin Lebanon.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa ta tilasta wa jirgin komawa da baya-baya bayan an harbe shi da makaman kariya masu hadarin gaske a yankin

Duk da bayanan da kungiyar Hisbullah ta yi, har zuwa lokacin hada wannan rahoton Isra’ila ba ta yi wani bayani a kan ikirarin harbo jirgin ba.

Magana kan sulhun Amurka da Iran

Tsohon Firaministan Qatar, Hamad bin Jassim bin Jaber Al Thani, ya ce wajibi ne ƙasashen Larabawa su samu ta cewa a kowace irin tattaunawa za a yi a tsakanin Amurka da Iran.

A yayin da ake ta jayayya kan rahotannin tattaunawa tsakanin Iran da Amurka — wanda Tehran ta musanta - Al Thani ya ce:

Kara karanta wannan

An fitar da bidiyon yadda rokokin Iran suka ruguza Isra'ila

“Ba zai yiwu ƙasashen GCC su kasance ba tare da wakilci ba a duk wani zaman sulhu da za a tsara a kan makomar yankin.”

A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, ya ce mashigar Hormuz ba kayan ciniki ba ne ko wata hanyar matsin lamba, kuma dole ne ya kasance a bude ba tare da wani sharadi ba.

Benjamin Netanyahu a wani waje da aka rusa a Isra'ila
Benjamin Netanyahu na duba wajen da Iran ta kai hari a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kai hari kasar Kuwait

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Kuwait ta ce an kai hari a filin jirgin sama, amma ba a samu wata babbar asara ko rasa rayuka ba.

Daga baya, Kuwait ta ce ta tare jirage marasa matuƙa guda shida da aka harba daga Iran duk da maganar sulhu da Donald Trump ke yi.

Jirgin sojojin Colombia ya yi hadari

A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun sojojin kasar Colombia sun gamu da wani mummunan hadarin jirgin sama a farkon makon nan.

Gwamnatin kasar ta sanar da cewa jirgin na dauke da mutane sama da 100, inda aka sanar da mutuwar mutum 64 da ke cikinsa.

Yayin da ake bincike, Shugaban kasar Colombia da ministan tsaron kasar sun tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng