Ba Sassauci: Iran Ta Ci Gaba da Luguden Wuta kan Isra'ila, Ta Farmaki Muhimman Wurare
- Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila
- IRGC ta kaddamar da rukuni na 80 na hare-haren ramuwar gayya kan muhimman wurare a Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka
- A cewar rundunar IRGC, hare-haren sun samu nasarar sauka a muhimman wurare inda suka yi barna mai girma
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da kaddamar da rukuni na 80 na hare-haren ramuwar gayya mai suna "Operation True Promise 4".
A wannan karon rundunar ta kai hari kan wasu muhimman wurare da cibiyoyin sojoji a yankin Arewacin Isra'ila, baya ga luguden wuta kan sansanonin Amurka da ke fadin yankin.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar a ranar Laraba, 25 ga watan Maris 2026.
Iran ta harba makamai kan Isra'ila
IRGC ta bayyana cewa dakarun da ke kula da sararin samaniya na rundunar ne suka kaddamar da wannan sabon rukuni na farmakin, tashar Aljazeera ta zo da labarin.
Ta ce an kaddamar da harin ne domin nuna goyon baya ga "hare-hare na alfahari" da kungiyar gwagwarmayar Hezbollah ta Lebanon ke kaiwa kan Isra'ila, da kuma mazauna Kudancin Lebanon wadanda suke fuskantar zaluncin Isra'ila.
Sanarwar ta ce:
"An rugurguza muhimman wurare da cibiyoyin sojoji da ke Arewacin Isra'ila sakamakon munanan hare-haren makamai masu linzami na dakarun sararin samaniya na IRGC."
Wace irin barna makaman suka yi?
IRGC ta bayyana cewa hedkwatar rundunar sojojin Isra'ila da ke birnin Safed, wadda ke da alhakin tsara hare-hare da tsaro a iyakokin Arewacin Isra'ila, tana daya daga cikin manyan wuraren da aka kai wa harin.
Sanarwar ta bayyana wadannan hare-hare a matsayin farkon jerin wasu ayyukan soja da aka riga aka sanar da za a yi kan "haramtacciyar gwamnatin Isra'ila mai kisan yara."

Kara karanta wannan
Rana ba ta karya: Halin da ake ciki yayin da ICPC ta gurfanar da El Rufai a gaban kotu

Source: Twitter
Za a ci gaba da kai wa Isra'ila hari
Rundunar ta ce za a ci gaba da kai munanan hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan wuraren taron sojojin Isra'ila a Arewa da kuma yankin Gaza.
IRGC ta ce ba za ta sassauta ko kadan ba yayin da take gudanar da wadannan hare-haren na ramuwar gayya.
Haka zalika, IRGC ta bayyana cewa an farmaki wurare a tsakiyar Isra'ila, ciki har da Tel Aviv, Kiryat Shmona, da Bnei Brak.
Makaman Iran sun yi barna a Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa makamai masu linzami da Iran ta harba sun yi nasarar sauka a wasu biranen Isra'ila.
Makaman masu linzami wadanda rundunar dakarun kare juyi juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta harba, sun sauka ne a birnin Bnei Brakinda suka raunata mutane tara.
Wani mazaunin yankin da ke kusa da daya daga cikin wuraren da makaman suka fada ya bayyana cewa ya ji karar da bai taba jin ta ba a rayuwarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
