Makaman da Iran Ta Harba Sun Gigita Isra'ila, an Ji Barnar da Suka Yi
- Iran kai hare-hare masu zafi kan Isra'ila ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka
- Makaman na Iran sun sauka a tsakiyar Isra'ila inda suka yi barna yayin da ake ci gaba da musayar wuta a tsakanin bangarorin da ke yakin
- Wani da ya samu ya shiga wajen fakewa kafin saukar makaman, ya bayyana cewa bai taba jin irin karar da ya ji ba a rayuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Makamai masu linzami da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba sun sauka a tsakiyar Isra'ila.
Makaman sun sauka ne a ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026 inda suka raunata mutane tara.

Source: Getty Images
Jaridar The Times of Israel ta ce jami'an agajin gaggawa sun bayyana cewa mutanen sun jikkata ne a garin Bnei Brak.
Ana musayar wuta tsakanin Iran, Isra'ila
Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce ta kai hari kan wata muhimmiyar masana'antar kera abubuwan fashewa ta Iran a yankin Isfahan, yayin da Iran kuma ta zargi Amurka da Isra'ila da kai hari tashar nukiliyarta ta Bushehr.
Wadanda suka ji rauni a Bnei Brak sun hada da wani matashi dan shekara 23 wanda ke cikin yanayi mai tsanani, da wasu mutane takwas, jaridar Haaretz ta kawo labarin.
Makaman Iran sun firgita jama'a
Wani mazaunin yankin da ke kusa da daya daga cikin wuraren da bam din ya fada ya bayyana cewa ya ji karar da bai taba jin ta ba a rayuwarsa.
"Mun shiga cikin dakin fakewa sai mu ka ji wani karar fashewa wanda ban taba jin irinsa ba a rayuwata."
"Mun gani ta taga hanyar ta cika da baraguzai da hayaki. Abin tsoro ne kwarai. Kunnuwa na sai amsa kuwwa suke yi."
- Wani mazaunin yankin
Jami'an ceto sun bayyana cewa sauran kananan bama-baman sun fada a Petah Tikva, Givat Shmuel, da Rosh Haayin, inda suka haddasa barna amma ba su jikkata kowa ba.
Wasu mutane sun raunata
Wannan hari shi ne na 12 daga cikin jerin hare-haren makamai masu linzami guda 13 da Iran ta harba wa Isra'ila a ranar Talata.

Source: Twitter
Akalla mutane tara, ciki har da yara biyu, ne suka ji rauni a sassan kasar sakamakon hare-haren farko da aka kai a cikin ranar.
Daga bisani, makamai masu linzami na Iran da aka harba a daren Laraba sun sa an kunna kararrawar gargadi a birnin Eilat da ke kudancin kasar, da kuma yankunan Jerusalem da tsakiyar Isra'ila, kodayake ba a bayar da rahoton samun raunuka kai-tsaye ba.
Hukumar MDA ta ce jami'an lafiya sun duba mutane da dama da suka ji rauni yayin gudu zuwa dakunan fakewa ko kuma wadanda suka firgita sosai.
An soki gwamnatin Netanyahunkan yaki da Iran

Kara karanta wannan
Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Firaministan Isra'ila, Ehud Barak, ya ragargaji gwamnatin Benjamin Netanyahu.
Ehud Barak ya soki jami'an gwamnatin kasar inda ya zarge su da yaɗa karya a fili game da yaƙi da Iran, inda ya nuna cewa gwamnatin ba ta da wani tsari na kawo ƙarshen yakin.
Hakazalika, tsohon Firaministan ya nuna cewa iƙirarin gwamnatin na kawar da barazanae Iran ba ta yi daidai da gaskiyar lamarin ba.
Asali: Legit.ng

