Saudiyya Ta Yi Abin da ba a Yi Tsammani ba, Ta Nemi Alfarmar Trump kan Iran
- Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana yakin Iran a matsayin wata babbar dama ta sauya siyasar yankin Gabas ta Tsakiya gaba daya
- Saudiyya ta karyata zargin ingiza Amurka zuwa yaki, inda tace babban burinta shine kare jama'arta daga hare-haren jiragen mara matuka
- Donald Trump ya ce ana tattaunawa mai kyau da Iran, amma mahukuntan Tehran sun karyata batun tattaunawar yayin da ake fafatawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Saudiyya - Rahoto ya nuna cewa yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya kasance yana matsa wa Shugaba Donald Trump lamba domin Amurka ta ci gaba da yakin da take yi da Iran.
A cewar majiyoyi da suka san da tattaunawar, Yarima Salman ya shaida wa Trump cewa wannan yakin wata “babbar dama ce” wadda za a yi amfani da ita wajen sake fasalin siyasar Gabas ta Tsakiya baki daya.

Source: Getty Images
Yariman Saudiyya na tunzura Trump
A cikin jerin tattaunawar da suka yi a makon jiya, Yarima Salman ya jaddada cewa dole ne Amurka ta matsa kaimi har sai an ruguza gwamnatin Musulunci ta Iran, in ji rahoton New York Times.
A cewarsa, Iran tana zaman babbar barazana ga yankin Tekun Fasha, kuma “hanya daya tilo da za a yi maganinta ita ce kakkabe gwamnatin kasar gaba daya.”
Duk da cewa Firayim Minista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ma yana kallon Iran a matsayin barazana, akwai sabanin fahimta tsakanin Saudiyya da Isra'ila.
Manazarta sun ce Isra'ila na iya mayar da wukarta a kube idan Iran ta tsinci kanta a rikicin cikin gida ta yadda ba za ta iya tsole idon makiyanta ba, amma Saudiyya tana ganin hakan a matsayin 'an kashe maciji ba a sare kansa ba,' don haka, kawo karshen gwamnatin kasar shi ne mafita.
Saudiyya ta musanta tunzura Amurka
A gefe guda, gwamnatin Saudiyya ta fito ta karyata cewa ita ce take ingiza Amurka zuwa yakin da ba shi da karshe da kasar Iran.
A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce:
“A koyaushe, masarautar Saudiyya ta kasance tana goyon bayan hanyoyin zaman lafiya wajen warware wannan rikici, tun kafin ma a fara shi.”
Sun kara da cewa babban abin da ya dame su a yanzu shi ne "kare kanmu daga hare-haren yau da kullum da ake kai wa jama’armu da gine-ginenmu na farar hula.”

Source: Getty Images
Musayar yawu tsakanin Trump da Iran
Shugaba Donald Trump dai ya fito ya bayyana cewa gwamnatinsa da Iran sun yi “ingantacciyar tattaunawa game da kawo karshen yakin baki daya,” kodayake Iran ta karyata cewa ana yin wata tattaunawa a halin yanzu.
Saudiyya ta zargi Iran da cewa “ta zabi yin kasada da rayukan jama'arta maimakon bin hanyoyin diflomasiyya na gaskiya,” lamarin da suka ce yana cutar da kowa, musamman ma ita kanta kasar Iran din, in ji rahoton Daily Mail.
Duk da Trump ya nuna alamun son kawo karshen yakin a wasu lokutan, Yarima Salam ya bayyana hakan a matsayin kuskure, inda yake matsa kaimi wajen ganin an kai hare-hare kan matatun makamashin Iran.
Trump ya fasa kai hari kan Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ba sojojin Amurka umarnin dakatar da kai hare-hare kan matatun mai da wutar lantarkin Iran.
A cewar Donald Trump, dakatarwar ta tsawon kwanaki biyar ce kacal, yayin da ya ce Amurka na kan teburin tattaunawa da Iran a yanzu haka.
Wannan sanarwa ta kawo sauki ga fargabar karancin makamashi a duniya, biyo bayan rufe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta yi a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng


