Ana cikin Yaki da Iran, an Fallasa Karyar da Netanyahu Yake Yi a Isra'ila
- Tsohon Firaministan Isra'ila, Ehud Barak, ya fito ya ragargaji gwamnatin Benjamin Netanyahu kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Ehud Barak ya zargi gwamnatin da rashin bayyana gaskiya kan yakin da ake yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Tsohon Firaministan ya nuna cewa abubuwan da gwamnatin ta ke gaya masu, ba su ba ne gaskiyar hakikanin abin da ke faruwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Tsohon Firaministan Isra'ila, Ehud Barak, ya caccaki gwamnatin Benjamin Netanyahu.
Ehud Barak ya soki shugabannin siyasa da na soji na gwamnatin yanzu, inda ya zarge su da yaɗa karya a fili game da yaƙi da Iran, sannan ya lura cewa gwamnatin ba ta da wani tsari na kawo ƙarshen yaƙin.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce Ehud Barak ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi.
An caccaki gwamnatin Netanyahu
Ehud Barak, wanda kuma ya taba zama babban jami'an sojoji kuma Ministan harkokin tsaro na ƙasar, ya yi tsokaci game da yaƙe-yaƙen Isra'ila a Gaza, Labanan, da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
"Ba za mu iya buɗe Mashigar Hormuz ba, haka kuma ba za mu iya lalata ƙarfin nukiliya da na makamai masu linzami na Iran ba, don haka kada ku riƙa yi mana ƙarya da yawa."
- Ehud Barak
Ehud Barak, wanda ya yi aiki a matsayin Firaminista daga 1999 zuwa 2001, ya caccaki majalisar yaƙin ƙasar, inda ya jaddada cewa ɓangaren siyasa ba shi da ko nufin kawo ƙarshen fafatawar da ta kasa cimma kowane irin buri, Radio 786 ya saka labarin a Facebook.
"Isra'ila a matakin siyasa ba ta sani ba, ko dai ba ta sani ba ko kuma ba ta so ta kawo ƙarshen yaƙin. Ba su san yadda ake kammala yaƙe-yaƙe ba."

Kara karanta wannan
An zo wajen: Trump ya yi magana kan tsagaita wuta a yakin Amurka, Isra'ila da Iran
- Ehud Barak
An zargi Netanyahu da yin karya
Ya kuma yi nuni da alƙawuran da ba su cika ba waɗanda gwamnatin Benjamin Netanyahu ta sha yi game da yaƙe-yaƙen kisan kiyashi a Gaza da Lebanon.
“Shekaru biyu da rabi ke nan, Hamas tana nan bayan sun yi mana alƙawari har sau shida cewa an kusa samun 'cikakkiyar nasara.' Hezbollah tana nan bayan sun gaya mana cewa mun mayar da su baya da shekaru da dama."
- Ehud Barak

Source: Getty Images
Ehud Barak ya kuma soki yadda Netanyahu ya daɗe yana jaddada abin da ake kira "barazanar Iran," inda ya nuna cewa iƙirarin gwamnatin na kawar da hatsarin bai yi daidai da gaskiyar lamarin ba.
"Shirin nukiliyar Iran da makamai masu linzami har yanzu suna nan bayan sun fayyace mana cewa shi [Netanyahu] ya kawar da barazanar da ke barazana ga rayuwarmu."
- Ehud Barak
Sojojin Isra'ila sun harbi dan kasarsu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Isra'ila sun yi kuskuren bude wuta kan wani dan kasar wanda hakan ya jawo mutuwarsa.
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa harsasan makaman atilare na sojojin Isra'ila ne suka samu mutumin bisa kuskure.
Hakazalika, binciken ya nuna cewa an harba makaman ne da nufin bayar da kariya ga dakarun Isra'ila dake fafatawa a Kudancin Lebanon.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

