Dara Ta Ci Gida: Sojojin Isra'ila Sun Yi Kuskure, Sun Harba Makami kan Mutanensu
- Binciken sojojin Isra'ila ya tabbatar da cewa dakarun kasar ne suka kashe wani manomi dan shekaru 60 a bisa kuskure a ranar Lahadi
- Sojojin sun amince cewa kuskure suka samu wajen saita makaman atilare da suka harba don kare yankin Misgav Am daga harin Hezbollah
- Janar Rafi Milo ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici sosai duba da cewa sojojin ne suka kashe mutumin da ya kamata su kare
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lebanon - Wani binciken gaggawa da rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta gudanar ya bankado yadda wani dan kasarsu, Ofer Moskovitz, ya mutu a kwanakin baya.
Binciken ya nuna cewa ba makaman Hezbollah ne suka kashe Moskovitz, wani manomi mai shekaru 60 yayin da yake tuka motarsa a yankin Misgav Am ba.

Source: Getty Images
Sojojin Isra'ila sun yi kuskure a harin Lebanon
Maimakon haka, binciken ya tabbatar da cewa harsasan makaman atilare na sojojin Isra'ila ne suka same shi bisa kuskure a ranar Lahadi, in ji rahoton Wall Street Journals.
Wannan lamari ya tayar da kura a cikin rundunar sojin, inda aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan kurakurai na harbin kuskure tun bayan barkewar yakin kasar da Hezbollah.
Rundunar sojin ta bayyana cewa binciken, wanda kwamandan shiyyar Arewa, Janar Rafi Milo, ya jagoranta tare da wasu manyan hafsoshi, ya gano "kurakurai masu tsanani na aiki" a harin.
Rahoton binciken ya nuna cewa an harba makaman ne da nufin bayar da kariya ga dakarun Isra'ila dake fafatawa a kudancin Lebanon.
An kashe manomi a harin kuskuren Isra'ila
Sai dai, sakamakon kuskuren lissafi na inda aka saita bindigogin, harsasai biyar suka sauka a kan tsaunin Misgav Am, maimakon wuraren 'makiya' da aka nufa.
Hukumar agajin gaggawa ta Magen David Adom ta bayyana cewa harbin ya haddasa wata gagarumar gobara da ta cinye motoci biyu, in ji rahoton The TImes of Israel.

Kara karanta wannan
Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya
Jami'an agajin ne suka ciro gawar Moskovitz daga cikin daya daga cikin motocin bayan kashe gobarar. Abin mamaki a nan shi ne, babu wata kararrawar gargadi da aka kunna kafin harsasan su fada yankin, wanda hakan ya hana mazauna yankin samun damar neman mafaka.

Source: Getty Images
Martanin sojoji da iyalan wanda aka kashe
Janar Rafi Milo ya bayyana lamarin a matsayin "abin da ya yi muni sosai," inda ya ce babban abin takaicin shi ne mutumin ya mutu ne sakamakon harbin dakarun da aka tura domin su kare shi da yankinsa.
Rundunar ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan Moskovitz da kuma daukacin mazauna karkara ta Misgav Am, tare da alkawarin gudanar da karin bincike mai zurfi wanda za a gabatar wa iyalai da kuma jama'a.
Duk da wannan mummunan kuskure, dan uwan mamacin, Roni Moskovitz, ya koka kan yadda sojojin ba su yi magana da iyalan kai-tsaye ba, inda ya ce sun ji sakamakon binciken ne kawai ta hannun shugabannin karkarar tasu.
Halin da ake ciki a Isra'ila bayan harin Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, kasar Isra’ila ta ayyana dokar ta-baci bayan Iran ta harba makamai masu linzami wanda ya jawo hana yawan taruwar mutane.
An kwashe marasa lafiya zuwa karkashin kasa a asibitoci yayin da aka kira sojojin ajiyar gaggawa domin kare iyakoki daga hare-haren makamai.
Duk da barazanar, wasu mazauna Tel Aviv sun nuna kwarin gwiwa da tsarin kariya na iska, suna goyon bayan matakin soja na Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

