Yakin Iran: IEA Ta Bayyana Matsalar da Tattalin Arzikin Duniya zai Fuskanta

Yakin Iran: IEA Ta Bayyana Matsalar da Tattalin Arzikin Duniya zai Fuskanta

  • Hukumar da ke kula da makamashi ta duniya, IEA ta hanga babbar matsala da ke tunkarar duniya saboda yaki da Iran
  • Yakin da Amurka da Isra'ila suka jawo da Iran ya fara daukar sabon salo bayan an fara kai hare-hare kan makamashi
  • Hukumar ta bayyana cewa a yanzu haka ta fara daukar sababbin matakai da za su taimaka wajen rage girman matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Shugaban hukumar kula da makamashi ta duniya, IEA, Fatih Birol, ya gargadi cewa tattalin arzikin duniya na fuskantar babbar barazana.

Ya bayyana cewa za a samu wannan matsala ne sakamakon rikicin makamashi daga yakin da ake yi da Iran.

IEA ta yi gargadi game da yakin Iran Amurka da Isra'ila
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei (hagu) da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Anadolu & Win McNamee
Source: Getty Images

TRT World ta wallafa cewa da yake jawabi a taron manema labarai na kasa da kasa a Canberra, babban birnin Australia, Birol ya kwatanta wannan rikici da matsalolin makamashi na shekarun 1970.

Kara karanta wannan

Manya: Najeriya za ta warware matsalar da yakin Iran da Amurka ta haifar

IEA ta yi magana kan yakin Iran

Aljazeera ta ruwaito cewa a cewarsa, rikicin da ake ciki yanzu ya hada matsalolin mai da kuma durkushewar iskar gas.

Fatih Birol ya ce lamarin na kara tsananta matsin lamba ga kasuwannin duniya. Ya jaddada cewa idan aka ci gaba da tafiya a wannan hanya, babu wata kasa da za ta tsira daga illar wannan rikici.

Faith Birol ya kara da cewa akwai bukatar hadin gwiwar kasashen duniya domin shawo kan matsalar cikin gaggawa, yana mai fatan za a samu mafita nan ba da jimawa ba.

Amurka, Isra'ila da Iran sun fara kai hare-hare kan wuraren makamashinsu
Wuta ta tashi a yayin harin da ake kai wa tsakanin kasashen Gabas ta Tsakiya Hoto: @Iran
Source: Twitter

Yayin da yakin ke shiga mako na hudu, Shugaban Amurka Donald Trump da gwamnatin Iran na ci gaba da yin barazana ga juna.

Shugaban na Amurka ya bukaci a bude mashigar Hormuz, wadda kusan 20% na jigilar mai da iskar gas na duniya ke bi ta cikinta.

Ana fuskantar barazana kan yakin Iran

Sai dai toshewar wannan mashiga ta Hormuz ya kusa dakatar da jigilar man fetur gaba daya, lamarin da ya haddasa tashin farashin mai a kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Amurka ta fara neman $200bn don ci gaba da farmakin Iran

A bangare guda kuma, shugaban IEA ya bayyana cewa suna tattaunawa da gwamnatocin kasashen Asiya da Turai kan yiwuwar sakin karin ajiyar mai idan bukatar hakan ta taso.

Ya ce za su duba yanayin kasuwa tare da tuntubar kasashen da ke cikin hukumar kafin a hadu wajen daukar matakin da ya dace.

A ranar 11 ga watan Maris, kasashen IEA sun amince da sakin ganga miliyan 400 na mai daga ajiyar gaggawa domin rage tashin farashin mai a duniya.

Sai dai Birol ya bayyana cewa babu wani takamaiman matakin farashin mai da zai tilasta sake daukar irin wannan mataki.

Ya bayyana rikicin Gabas ta Tsakiya a matsayin mai matukar tsanani, yana mai gargadin cewa sakamakonsa na iya shafar dukkannin bangarorin tattalin arzikin duniya.

Yakin Iran: Amurka na neman karin kudi

A baya, mun wallafa cewa Pentagon na neman karin kudi domin ta samu damar ci gaba da kai hare-hare a yakin da ta shigar wa Isra'ila a kan Iran.

Rahotanni sun tababtar da cewa Amurka tana tafka mummunar asara bayan Iran ta rikakai hari kan kadarorinta a Gabas ta Tsakiya bayan ta hada kai da Isra'ila.

Ana hasashen za a samu rikici mai zafi a majalisar dokokin Amurka saboda yawn kudin da ma'aikatar tsaron ta ke nema don ci gaba da yakin da wasu ke adawa da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng