Makaman Iran Sun Razana Netanyahu, Ya Fito a Bidiyo Yana Neman Agaji

Makaman Iran Sun Razana Netanyahu, Ya Fito a Bidiyo Yana Neman Agaji

  • Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya fito ya yi magana a wani bidiyo yana neman kasashen duniya su shiga yakin da suke da Iran
  • Netanyahu ya yi korafi ne bayan wasu zafafan hare-hare da Iran ta kai Isra'ila, lamarin da ya jikkata kusan Yahudawa 200 da rusa gine-gine
  • Biyo bayan kiran Netanyahu, Birtaniya ta karyata ikirarin da Firaministan Isra'ila ya yi game da karfin makaman da kasar Iran ta mallaka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi cewa Iran na da karfin kai hari har cikin nahiyar Turai, inda ya bukaci shugabannin duniya su dauki mataki.

Netanyahu ya yi kiran ne yayin da ya ziyarci wurin da makami mai linzami daga Iran ya fadi a birnin Arad da ke Kudancin kasar a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Ba da yawun mu ba," Birtaniya ta kware wa Shugaba Trump baya a yaki da Iran

Benjamin Netanyahu a Arad
Benjamin Netanyahu a wajen da Iran ta kai hari a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar Benjamin Netanyahu kan karfin Iran

Rahoton tashar Iran International ya nuna cewa Benjamin Netanyahu ya ce Iran na da karfin makamai da za ta iya harbawa kasashen Turai.

Netanyahu ya ce:

“Suna da karfin isa har cikin Turai sosai. Suna iya sa kowa cikin jerin hare-harensu.”

Ya kara da cewa, idan ana bukatar hujja cewa Iran na barazana ga duniya baki daya, abubuwan da suka faru cikin awanni 48 da suka gabata sun tabbatar da hakan.

Firaministan ya kuma zargi Iran da harba makamai masu linzami zuwa birnin Jerusalem kusa da wuraren ibada masu muhimmanci.

A cewarsa, Iran ta kai hari da makami mai linzami mai nisa zuwa Diego Garcia, wanda ke da nisan kimanin kilomita 4,000, yana mai cewa hakan na nuna cewa yanzu suna da karfin kai hari har cikin manyan biranen Turai.

Netanyahu ya nemi agajin duniya

Netanyahu ya kuma zargi Iran da kai hare-hare kan fararen hula da wuraren ibada, ciki har da bangon Western Wall, cocin Holy Sepulcher da kuma masallacin Al-Aqsa.

Kara karanta wannan

Manya: Najeriya za ta warware matsalar da yakin Iran da Amurka ta haifar

Bugu da kari, Firaministan ya ce Iran na kawo cikas ga zirga-zirgar makamashi a duniya ta hanyar tasirinta a mashigar ruwan Hormuz.

Wani jirgi da ya nufi hanyar ruwan Hormuz
Jirgin ruwa ya nufi mashigar Hormuz a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Saboda haka ya bukaci shugabannin duniya su hada kai da Amurka da Isra’ila domin fuskantar Iran, yana mai cewa barazanar ta wuce yankin Gabas ta Tsakiya kawai.

Ga bidiyon Netanyahu da gwamnatin Isra'ila ta wallafa a X:

Martanin Birtaniya ga Netanyahu

Sai dai a daya bangaren, wani minista a Birtaniya, Steve Reed, ya ce babu wata sahihiyar hujja da ke nuna cewa Iran na shirin kai hari ga Turai da makamai masu linzami ko kuma tana da wannan karfi.

Rahoton Jerussalem Post ya nuna cewa Reed ya kara da cewa babu wani bincike da ya tabbatar da irin ikirarin da Netanyahu ya yi.

Iran: Amurka ta aika sako da Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta aika sako na musamman ga Isra'ila game da yakin da aka fara a karshen watan Fabrairun 2026.

Amurka ta sanar da gwamnatin Benjamin Netanyahu cewa yakin da ake da Iran zai dauki tsawon lokaci fiye da yadda aka yi tsammani a farko.

Wani rahoto ya nuna cewa kasar Amurka za ta iya kaiwa har watan Satumban 2026 ana fafatawa da ita ko da kuwa yakin ya dan lafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng