Netanyahu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Ziyara zuwa Hungary Zai Iya Jefa Shi a Matsala

Netanyahu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Ziyara zuwa Hungary Zai Iya Jefa Shi a Matsala

  • Hukumar kare hakkin dan Adam ta 'Human Rights Watch' ta bukaci Hungary ta kama Benjamin Netanyahu idan ya ziyarci kasar
  • Kotun hukunta manyan laifuffuka ta ICC ta bayar da sammacin kama Netanyahu da Yoav Gallant kan zargin laifuffukan yaki da na bil’adama a Gaza
  • Kungiyar ta zargi Viktor Orbán da karya doka, tare da kira ga EU ta dauki mataki kan rashin bin umarnin kotun ICC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Kungiyar 'Human Rights Watch' ta ce ya kamata hukumomin Hungary su kama Benjamin Netanyahu.

Hukumar ta yi wannan kira ne yayin da Netanyahu ke shirin shiga kasar domin ziyara, saboda sammacin kotun ICC.

An bukaci cafke Netanyahu kan ta'addanci a duniya
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya karbi bakuncin takwaransa na Hungary, Viktor Orban a Jerusalem a 2018. Hoto: Debbie Hill/AP.
Source: Getty Images

An bukaci ICC ta cafke Benjamin Netanyahu

Ana sa ran Netanyahu zai ziyarci Hungary domin halartar wani taron siyasa, yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu mai zuwa, kamar yadda hukumar ta wallafa a X.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta jawo wa kanta, Rasha ta shiga kafar wando daya da ita kan hari a Lebanon

A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, kotun ICC ta fitar da sammacin kama Netanyahu tare da Yoav Gallant kan zargin laifuka.

Ana zargin su da aikata laifukan yaki da na bil’adama a Gaza tun daga watan Oktoba, 2023, kuma har yanzu suna gujewa gurfana gaban kotu.

Kasashen da ke cikin ICC na da alhakin kama duk wanda ake nema idan ya shiga yankunansu, duk da cewa Hungary na kokarin ficewa daga kotun.

Wata jami’ar bincike, Alice Autin, ta ce rashin bin wannan doka na kara karfafa rashin hukunta masu laifi tare da cin zarafin wadanda aka cutar.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta caccaki Netanyahu kan ta'addanci a duniya
Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Ziyarar Netanyahu na zuwa ne a lokacin da ake fama da rikici tsakanin Isra’ila da Iran, inda ake kai hare-hare masu yawa tsakanin bangarorin biyu.

Haka kuma, Isra’ila ta kara hare-hare a Lebanon tare da tilasta mutane kaura daga gidajensu, lamarin da ka iya zama laifin yaki.

Zargin da ake yi wa sojojin Isra'ila

Tun daga 2023, ana zargin sojojin Isra’ila da aikata laifukan yaki da kisan kiyashi a Gaza, tare da hana shigar kayan agaji masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

Kasashe 5 da suka kira Iran ta waya, suka nuna ana tare bayan fara yaki da Amurka

A shekarar 2025, Netanyahu ya taba ziyartar Hungary amma ba a kama shi ba, lamarin da ya jawo suka daga kotun ICC.

Firaministan Hungary Viktor Orbán ya sanar da aniyar kasar na ficewa daga yarjejeniyar ICC, wadda za ta fara aiki a 2026.

Kungiyoyi da lauyoyi a Hungary sun soki wannan mataki, suna cewa yana barazana ga doka da adalci a cikin kasa.

Tun 2010, gwamnatin Orbán na fuskantar zargi kan tauye ‘yancin kotuna, kafafen yada labarai, da kungiyoyin fararen hula.

Kungiyar ta kuma ce Tarayyar Turai ba ta dauki matakin da ya dace ba wajen dakile matakan Hungary na karya doka.

A karshe, an bukaci kasashen EU su matsa lamba ga Hungary ta bi dokokin ICC tare da kama Netanyahu idan ya shiga kasar.

Rasha ta gayyaci jakadan Isra'ila

A baya, an ji cewa Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta gayyaci jakadan Isra’ila Oded Joseph saboda ya yi mata karin bayani kan harin da aka kai a Lebanon.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Isra'ila ta kai wani hari ya jikkata ‘yan jaridar RT a kasar Lebanon a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Jakadan Isra’ila ya ki yin tsokaci ga manema labarai kafin ganawa a Moscow, yana mai cewa ba ya son makara yayin da ake jiran bayani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.