Saudiyya, ƙasashen Musulmi Sun Fara Jin Haushin Isra'ila kan Hari a Ƙasar Larabawa
- Kasashen Larabawa ciki har da Saudiyya da Turkiyya sun yi Allah wadai da harin Isra’ila kan Syria a yankin Gabas ta Tsakiya
- Larabawan sun yi kira ga duniya ta dauki matakin gaggawa kan Isra'ila saboda saba dokokin kasa da kasa da ta ke yi
- Isra’ila ta ce harin ya biyo bayan kai hare-hare kan kabilar Druze a Sweida, yayin da Syria ta zargi kasar da karya dokokin kasa da kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudi Arabia - Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta yi Allah wadai da harin Isra’ila kan sansanonin sojin Syria yayin da ake yaki tsakanin kasar da Iran.
Kasashen Larabawa sun hada kai domin sukar harin Isra'ila da suka ce ya saba dokokin kasa da kasa da wanda ke bukatar daukar matakan gaggawa.

Source: Twitter
Syria: Kasashen Larabawa sun dura kan Isra'ila
Rahoton Anadolu Ajansi ya ce harin abin takaici ne inda suke kiran hakan da “ta’addanci” da ya saba dokokin kasa da kasa.
Har ila yau, ƙasashen sun bukaci duniya ta dauki mataki kan Isra'ila saboda ta'addancin da take yi.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai harin ne a kudancin Syria bayan hare-haren da aka kai kan kabilar Druze a lardin Sweida, suna cewa suna kare wannan karamar al’umma.
Kasashen Larabawa kamar Turkiyya, Masar, Jordan, Qatar da Kuwait sun bayyana harin a matsayin barazana mai tsanani, suna jaddada bukatar kare ikon Syria da hana irin wadannan hare-hare.

Source: Getty Images
Bukatar ƙasashen ga Majalisar Dinkin Duniya
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen hare-haren Isra’ila da take yi a Syria.
Rahotanni sun ce rikice-rikice a Sweida sun kashe akalla mayakan Druze hudu, yayin da harbe-harben Isra’ila suka afkawa unguwannin fararen hula a birnin.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta jawo wa kanta, Rasha ta shiga kafar wando daya da ita kan hari a Lebanon
Gwamnatin Syria ta soki harin, tana cewa ya keta ikon kasa, yayin da shugaban kasar ya ce yana kokarin kaucewa shiga kowanne rikici a yankin, cewar rahoton Vanguard.
Hukumomin Syria sun riga sun bayyana cewa suna tabbatar da daidaito da hakkoki ga dukkan bangarorin al’umma, ciki har da kabilar Druze.
Sannan kasar ta zargi Isra’ila da amfani da batun Druze a matsayin hujjar tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Syria.
Wannan lamari ya kara bata alakar ƙasashen da Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki tsakaninta da Iran wanda wasu daga cikinsu ke mara mata ba.
Iran/Isra'ila: Kasashen Larabawa sun yi zama
An ji cewa yayin da yakin da Isra'ila da Amurka hada kai suka kaddamar a Iran ke cigaba da jawo asarar rayuka, shugabannin Musulmi sun yi zama.
Ma'aikatar harkokin kasar Saudiyya ta bayyana cewa an yi zaman a ranar 29 ga watan Ramadan, 1447 a babban birnin kasar, Riyadh.
Ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana cewa ya halarci zaman tare da sanar da wasu muhimman abubuwan da za su tattauna a tsakaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
