Amurka Ta Ji Wuya: Dole Ta Sanya Trump Yi wa Iran Abin Alheri

Amurka Ta Ji Wuya: Dole Ta Sanya Trump Yi wa Iran Abin Alheri

  • Yayin da ake tsaka da gwabza yaki, gwamnatin Donald Trump ta nufi Iran da alheri wajen janye takunkumi ga man fetur da kasar ke fitarwa
  • Hakan na zuwa ne yayin da farashin fetur, iskar gas da sauransu ke kara tashi a Amurka, lamarin da ke zama barazana ga siyasarTrump
  • An bayyana cewa lamarin zai kara ba Iran damar tara kudin shiga ta inda za ta kara hadawa da sayen makamai domin tunkarar Amurka/Isra'ila

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Gwamnatin Amurka ta cire takunkumi kan gangar mai miliyan 140 na Iran yayin da Donald Trump ke kokarin ganin farashin man fetur ya sauka a fadin kasarsa.

Rahotanni sun nuna cewa a daren Juma’a gwamnatin Trump ta ba Iran lasisi na wucin gadi domin sayar da man da ke cikin tankokin jiragen ruwa a teku.

Kara karanta wannan

Switzerland ta rufe ido, ta dakatar da sayar wa Amurka makamai kan yaƙi da Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump yana sauraron masu jawabi a wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta wallafa cewa hukumar makamashin Amurka ta ce man ya kai ganga miliyan 140, wanda ya isa ya wadatar da bukatar mai ta duniya gaba daya na kusan kwana daya da rabi.

Amurka ta shafe shekaru tana kakaba takunkumi kan man Iran lokaci zuwa lokaci, kuma gwamnatin Trump ta hana sayar da man kasar tun bayan da ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Tehran a 2018.

Ribar da kasar Iran za ta samu

Ana ganin cire takunkumin na tsawon wata guda na iya haifar da ce-ce-ku-ce a duniya yayin da Amurka/Isra'ila ke cikin yaki da Iran.

Sai dai masana sun ce hakan zai ba Iran damar sayar da man da aka kakaba wa takunkumi domin taimaka mata wajen daukar nauyin yakin da take yi da Amurka da kawayenta.

Mojtaba Khamenei yana sauraron jawabi
Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A yanzu haka dai China ce babbar mai sayen man Iran, kuma Tehran na barin jiragen ruwanta suna wucewa ta mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta ji wuta, za ta yi abin alheri ga jamhuriyar Musulunci ta Iran

Dalilin cirewa Iran takunkumin mai

BBC ta wallafa cewa farashin danyen mai ya tashi zuwa kusan Dala 110 kan kowace ganga a kasuwar duniya sakamakon yakin Iran da Amurka/Isra'ila.

Gwamnatin Trump na kokarin neman duk wata hanya da za ta rage farashin mai yayin da take ci gaba da yakin — ciki har da cire takunkumi kan miliyoyin gangar mai na Rasha a makon da ya gabata.

Wani rahoto ya ce ana hasashen za a bar Iran ta cigaba da sayar da mai bayan yakin tare da ba kasashen Turai damar sayensa ba China kadai ba.

Janye takunkumin ya samu yabo daga tsohon shugaban Bankin Duniya kuma jami’in Baitulmali a wa’adin farko na Trump, David Malpass wanda ya bayyana shi a matsayin:

“Mataki mai kyau na tattalin arziki.”

Iran ta harba makamai Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta harba makamai birnin Riyadh na Saudiyya bayan harin da aka kai mata a wajen da ta ke samar da gas.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Amurka ta fara neman $200bn don ci gaba da farmakin Iran

An ji saukar makaman Iran a daidai lokacin da kasashen Musulmi da Larabawa ke taro a Saudiyya domin shawo kan yakin da ake yi.

Gwamnatin Saudiyya ta yi Allah wadai da hare-haren tana mai cewa kamata ya yi Iran ta dauki matakin diflomasiyya ba kai hari ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng